You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814162

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

PSG na neman yi wa Man United maƙarƙashiya kan Hojlund

Rasmus Hojlund Rasmus Hojlund

Paris St-Germain ta yi tayin Yuro miliyan 50 kan dan wasan Atlanta da Manchester United ke zawarci Rasmus Hojlund.

Dan wasan na Denmark shi ne kan gaba a jerin wadanda kungiyar ta Old trafford ke nema ruwa a jallo a bana.

Erik ten Hag yana matukar bukatar kulla yarjejeniyar, inda United ta gamsu za ta iya sayen dan wasan mai shekaru 20 kafin wasansu na farko na gasar Premier da Wolves a Old Trafford ranar 14 ga watan Agusta. Sai dai a yanzu PSG ta bayyana sha'awar ta.

Ana tunanin yunkurin nasu na da nasaba da rashin tabbas na Kylian Mbappe.

Jami'an PSG dai sun hakikance cewa Mbappe ba shi da niyyar barin kungiyar a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa da ake yi a halin yanzu kuma ba za a yi nasara da tayin fam miliyan 259 da aka samu daga kulob din Al Hilal ta Saudiyya ba.