You are here: HomeAfricaBBC2023 04 19Article 1751672

BBC Hausa of Wednesday, 19 April 2023

Source: BBC

PSG na fatan ɗaukar Mourinho Man U da Liverpool na rububin Mac Allister

Jose Mourinho Jose Mourinho

Ɗan wasan gaban Tottenham daga Ingila Harry Kane mai shekara 29, shi ne babban burin ƙungiyar Paris St-Germain na samun ɗan gaba mai cin ƙwallo a lokacin kaka. (Le Parisien)

Hukumar gudanarwar Liverpool ta shirya kuma ta amince da wani kwanturagi ga ɗan wasan tsakiya na Ingila da ke buga wa Chelsea, ƙwallo wato Mason Mount ɗan shekara 24. (Football Insider)

Koci Jose Mourinho na iya zama manajan Paris St-Germain a kakar wasanni mai zuwa saboda mai horas da kulob ɗin na Roma a yanzu shi ne a sahun gaba cikin jerin mutanen da daraktan wasanni na PSG Luis Campos ke fatan ɗauka. (RMC Sport)

Akwai ƙarin yiwuwar koci David Moyes zai iya barin West Ham bayan kammala wannan kakar wasanni, yayin da shugabannin ƙungiyar suka fara ƙoƙarin tantance manajan da suke fatan zai maye gurbinsa. (Mail)

Crystal Palace na son Roy Hodgson ya ci gaba da zama a kulob ɗin har zuwa kakar wasanni ta gaba don ya riƙa bai wa duk mutumin da zai maye gurbinsa shawarwari. (Telegraph)

An ba da rahoton cewa Steven Gerrard yana cikin jerin koci-koci da kulob ɗin Olympiakos na ƙasar Girka ke son ɗauka, wata shida bayan ƙungiyar Aston Villa ta sallame shi. (Express)

Manchester United da Liverpool na kan gaba a rige-rigen ɗaukar ɗa wasan tsakiya na Brighton daga Argentina Alexis Mac Allister, an kasa samun wani ci gaba a tattaunawa kan matashin ɗan shekara 25 da Arsenal. (Cesar Luis Merlo - on Twitter)