You are here: HomeAfricaBBC2023 03 28Article 1739528

BBC Hausa of Tuesday, 28 March 2023

Source: BBC

PDP ta naɗa sabon shugaban riƙo na ƙasa

PDP ce jamiyyar adawa a Najeriya PDP ce jamiyyar adawa a Najeriya

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP ya amince da nadin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar na ƙasa.

A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya gudanar ranar Talata, ta ce ta ɗauki matakin ne domin biyayya ga hukuncin da babbar kotun jihar Benue ta yanke game da matayin shugabancin Iyochia Ayu.

Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba, ya ce bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la'akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban PDP mai kula da shiyyar arewacin ƙasar, Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam'iyyar.