You are here: HomeAfricaBBC2023 07 05Article 1798592

BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023

Source: BBC

PDP na zargin APC da neman tankware zaɓen shugabannin marasa rinjaye a majalisun Najeriya

PDP ce jamiyyar adawa a Najeriya PDP ce jamiyyar adawa a Najeriya

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce har yanzu ba ta cimma matsaya ba kan 'ya'yanta da za su yi shugabanci a majalisar dattawa.

PDP na shaida hakan ne adaidai lokacin da ake saran 'yan majalisar dattawa da wakilan kasar za su koma bakin aiki, bayan hutun babbar sallah a wannan Talatar.

Majalisar dai a wannan rana ake kuma sa ran za su zabi sauran shugabannin daga bangaren masu rinjaye da na marasa rinjaye.

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa da yiwuwar a yi zaɓen ko da PDP ba ta shirya ba.

'Gaza daidaitawa da 'ya'yanta'

Kafin wannan lokaci an yi tunanin PDP za ta shawo kan 'ya'yanta da ke neman kujerun marasa rinjiye a majalisun dokoki, musamman majalisar dattawa ta hanyar daidaita su da kuma tsayar da wanda take marawa baya a neman kujerun.

Sai dai bayan wani zama da shugabannin jam'iyyar suka yi da wasu daga cikin Sanatocin a ranar Litinin , abubuwa sun sake dagwule mata.

Sanata Abdul Ningi na PDP, ya shaidawa BBC cewa sun yanke shawarar cewa za a rubutu wa shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio wasika akan cewa kawo yanzu jam'iyyar ba ta cimma matsaya akan wadanda za su shugabanci majalisar ba.

"Mutane suna so fiye da daya ko uku, saboda haka kowa ya yi hakuri, za a fito da matakan da ya kamata a yi amfani da su wajan fidda wadanda za su shugabancin majalisar".

"Mu 'yan adawa ne ba ma neman hayaniya a cikin wannan zabe", in ji shi.

Jam’iyyar ta ce da zarar ta kamala aikinta za ta tura sunayen mutanen da ta tsayar.

Sai dai jam'iyyar PDP ta zargi APC mai mulki da shige mata hanci da kudundunewa, tana cewa APC na neman tankwara kujerun marasa rinjaye ta yadda sai wadanda take so daga ɓangaren marasa rinjaye ne za su dare.

Ta kuma ce wani abu ne da ba za ta lamunta da shi ba. Sai dai APC ba ta ce komai game da wannan zargi ba.

Bayanan da ke fitowa daga majalisar na nuna cewa komai ka iya faruwa, watakila a yi ta ta kare ko da PDP ta shirya ko ba ta shirya ba.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar wa BBC cewa da yiwuwar wasu daga cikin 'ya'yan PDP su bijire wa umurnin nata.

Ko za a iya zaɓen ba tare da samun tubarrakin PDP ba?

Bisa al'ada jam'iyyun siyasa ne ke da hurumin kasafta mukaman majalisu biyun a tsakanin 'ya'yansu.

Sai dai Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin siyasa a jami'ar Bayero ta Kano ya ce idan har aka gudanar da zaɓen ba tare da tubarrakin PDP ba, toh wannan ba zai bada mamaki ba.

"Misali mun ga yada ɓangaren zartarwa, ya shiga ya yi uwa ya yi makarɓiya wajan zaɓen shugabannin majalisu. Wannan a siyasar Najeriya abu ne mai yiwuwa ba, domin magana ce ta siyasar bukata ba siyasar akida ba".

Zaben na wannan Talatar dai yana da sarkakiya kasancewar bayan PDP, akwai wasu jam'iyyu da suka hada da NNPP da SDP da kuma YPP wadanda za su raba kujerun marasa rinjaye a tsakaninsu, kuma su ma ba a san gaban su ba.

Wannan ne ya sa masana ke cewa zaɓen shugabannin majalisar abu ne cikin duhu, sai a jira a ga yadda zata kaya.