You are here: HomeAfricaBBC2023 12 11Article 1896665

BBC Hausa of Monday, 11 December 2023

Source: BBC

Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka na 2023

Victor Osimhen Victor Osimhen

Dan wasan tawagar Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafarAfirka na 2023.

Dan wasan Super Eagles ya lashe kyautar a bikin da aka gudanar a Marrakech, wanda ya ja ragamar Napoli ta lashe Serie A karon farko bayan shekara 33.

Osimhen ya yi takara tare da dan wasan Morocco Achraf Hakimi da na Masar Mohamed Salah.

Dan wasan shi ne ya kai Super Eagles gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a badi, wanda ya ci kwallo 10 a karawar cancantar shiga gasar.

Osimhen ya ci kwallo 27 a dukkan fafatawa a Napoli, wadda ta koma kan ganiya a kwallon Italiya a kakar 2022-23.

Mai shekara 24 ya zama na farko a Napoli da ya zama kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Italiya tun bayan Diego Maradona a 1987/88.

Osimhen ya zama dan Najeriya na farko da ya lashe kyautar tun bayan Kanu Nwankwo a 1999.

A fannin mata Asisat Oshoala (Najeriya, Barcelona) ita ce ta lashe gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 20223.

Ta kuma yi takara tareda Thembi Kgatlana (Afirka ta Kudu, Racing Louisville) da kuma Barbara Banda (Zambia, Shanghai Shengli).