You are here: HomeAfricaBBC2023 12 08Article 1895288

BBC Hausa of Friday, 8 December 2023

Source: BBC

Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa a Italiya

Victor Osimhen Victor Osimhen

Dan wasan tawagar Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa a Italiya, bayan rawar da ya taka a ƙungiyar Napoli a kakar da ta gabata.

An karrama dan wasan na Super Eagles ranar Litinin, bayan da ya bayar da gudunmuwar da Napoli ta lashe gasar Serie A na farko bayan shekara 33.

Osimhen ya ci kwallo 26 a Serie A a kakar 2022-23, wanda ya sha gaban George Weah a tarihin yawan cin kwallaye a gasar.

Tsohon dan wasan Lille da Wolfsburg ya zama na farko a Afirka da ya lashe kyautar.

Wadanda suka karbi kyautar a baya-bayan nan sun hada da Zlatan Ibrahimovic da Andrea Pirlo da Cristiano Ronaldo da zakaran bara, Rafael Leao.

Osimhen na fama da jinya a kakar nan, amma matashin mai shekara 24 ya ci kwallo shida a wasa 10 da ya buga kawo yanzu.

Ya koma buga wasa a kungiyar da Walter Mazzari ke jan ragama a wasa da Atlanta ranar 25 ga watan Nuwamba, wanda ya canji dan kwallon.

Super Eagles za ta buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Ivory Coast tsakanin Janairu zuwa Fabrairun 2024 a Ivory Coast.

A fannin mata kuwa ƴar kasar Malawi, Tabitha Chawinga ita ce ta lashe kyautar, wadda ta ci kwallo 23 a Inter Milan.

Mai shekara 27, wadda ke buga wasannin aro a Paris St Germain, ta zama macen farko da ta lashe kyautar a gasar mata ta Italiya.

To sai dai Chawinga ba ta cikin 'yan takarar gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta bana.

Ranar 11 ga watan Disamba ne hukumar kwallon kafa ta Afirka, za ta sanar da gwarzuwar kwallon kafa ta bana a Marrakesh, Morocco.