You are here: HomeAfricaBBC2023 01 27Article 1703240

BBC Hausa of Friday, 27 January 2023

Source: BBC

Oshoala ta haskaka a yayin da Barcelona ta kafa tarihi a kwallon mata

Asisat Oshoala Asisat Oshoala

'Yar kwallon Najeriya, Asisat Oshoala ta nuna jin dadinta bayan da Barcelona ta lallasa Levante da ci bakwai da nema a wasan da Barca ta kafa tarihin samun nasara a wasanni 50 a jere.

Oshoala ta zura kwallo uku a wasan sannan ta bada kwallo daya aka ci.

Tawagar kwallon matan Barcelona ta samu galaba a wasanninta a jere kuma tun a watan Yunin 2021 rabon da wata kungiya ta doke ta.

"Na ji dadin zura kwallo uku a wasa daya kuma na taimaka wajen kafa wannan tarihin," in ji Oshoala.

"Abin alfahari ne ga kulob din kuma ina son in ci gaba da bayar da gudunmuwa wajen samun nasara."

Nasarar da Barcelona ta samu ya sa ta shiga gaban Lyon wacce a kwallon mata ta taba kafa tarihin nasara a wasa 46 a jere tsakanin 2011 zuwa 2014.

Tsohuwar 'yar kwallon Liverpool da Arsenal, Oshoala ta ce tana jin dadin yadda ta taka rawa a wannan tarihin da suka kafa.