You are here: HomeAfricaBBC2023 08 17Article 1826915

BBC Hausa of Thursday, 17 August 2023

Source: BBC

Olise ya tsawaita kwantiragi duk da Chelsea na zawarcinsa

Dan wasan Crystal Palace Michael Olise Dan wasan Crystal Palace Michael Olise

Dan wasan Crystal Palace Michael Olise ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya ta tsawon shekara hudu da kungiyar duk da cewa Chelsea na zawarcinsa.

A ranar Talata, an ba da rahoton cewa kulob din Stamford Bridge na nazarin biyan kudin sakin dan wasan da ya kai fam miliyan 35.

Amma shugaban Crystal Palace Steve Parish ya tabbatar a ranar Alhamis cewa dan wasan mai shekaru 21 zai ci gaba da zama a kungiyar.

Olise ya koma Palace daga Reading kan yarjejeniyar shekaru biyar a 2021 amma da farko ya kasance cikin tsarin matasa na Chelsea kafin ya bari ya na da shekaru 14.

Dan wasan ya taka rawar gani a kakar wasan da ta gabata inda ya ci kwallo biyu sannan ya taimaka sau 11 a wasanni 37 da ya buga, inda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara a kulob din.

A halin yanzu yana murmurewa daga raunin da ya ji a kafarsa da ya yi wa Faransa wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai na ‘yan kasa da shekara 21.