You are here: HomeAfricaBBC2021 03 22Article 1211944

BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Nowruz: Yadda Farisawa a sassan duniya ke bikin sabuwar shekararsu

Wannan shekara a kalandar Farisa ita ce ta 1400 Wannan shekara a kalandar Farisa ita ce ta 1400

Miliyoyin mutane a faɗin duniya sun yi bikin Nowruz - bikin murnar sabuwar shekarar Farisawa da kuma murnar shiga lokacin bazara.

Nowruz yana farawa ne daga lokacin bazara, lokacin da yini da dare suka kasance daidai.

Ana gudanar da bikin sabuwar shekarar ne galibi a Iran da Afghanistan da yankunan Kurdawa na Iraƙi da Turkiya da Indiya da wasu mazauna ƙasashen waje a sassan duniya.

Wannan shekarar - a kalandar Farisa ita ce ta 1400 - an gudanar da biki a wurare da dama duk da dokokin taƙaita yaɗuwar korona.

A wani dogon ɗakin asibitin Firoozabadi a Tehran, jami'an lafiya sun yi bikin ne tare da majinyata, inda suka ƙawata teburi da kayan abinci.

A dandalin Tajrish, ɗaya daga cikin wuri mafi cunkosu a Tehran, mutane suna sayen abinci da sauran kayayyaki daga kasuwa.

Bisa al'ada a Iran, mutane suna yi wa teburin Nowruz ado da wasu abubuwa - kamar kifi, ganyen alkama, kyandir da madubai.

A Turkiya, dubban Ƙurdawa ne suke cashewa da kaɗe-kaɗe da rawa a Santanbul.

Farisawan Indiya suna zuwa wurin ibadarsu a ranar bikin sabuwar shekarar. A nan, wani uba ne tare da ɗansa kan hanyarsu da zuwa wurin ibada a Tardeo da ke Mumbai.

A Srinagar, yankin Kashmir da ke ƙarƙashin Indiya, suna gudanar da al'adu a bikin Nowruz duk shekara, inda ake amfani da wasu halittu da ke shan jinin mutanen da ke neman maganin wata matsala ta lafiya.

Bayan faɗuwar rana musamman a garin Akra yankin Ƙurdawa na Iraƙi, mutane suna gudanar da wasan wuta.

Dukkanin hotunan suna da haƙƙin mallaka.