You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811897

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Nottingham Forest ta kammala daukar Elanga daga Man United

Anthony Elanga Anthony Elanga

Nottingham Forest ta sayi dan wasan gaban Sweden, Anthony Elanga daga Manchester United kan kwantiragin shekaru biyar.

Dan wasan mai shekaru 21 ya koma Old Trafford, wanda ake cewa Forest ta biya United fan miliyan 15.

Elanga ya kasance tare da United tun yana dan shekara 12, ya samu nasara a kungiyar a shekarar 2021, inda ya buga wasa 55 kafin Forest ta fara zawarcinsa.

Elanga ya kasance tare da tawagar United da ke Amurka don shirin tunkarar kakar bana.

Shine na biyu da Forest ta dauka kan fara kakar bana, bayan Ola Aina.

Ya koma kungiyar Steve Cooper duk da kungiyoyin Jamus da Everton sun so daukar dan wasan.

Elanga ya ci wa United kwallo hudu, ko da yake ya kasa zura kwallo a wasa 26 a kakar da ta wuce, wanda aka fara wasa da shi a karawa bakwai.