You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817393

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Nijar ta fara fuskantar katsewar wutar lantarki daga Najeriya

wayoyin wutar lantarki wayoyin wutar lantarki

Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar da kuma sauran wasu manyan birane kamar Maraɗi da Zinder sun fara fuskantar katsewar wutar lantarki.

Mutane na samun wutar lantarki na ne na tsawon kimanin sa'a ɗaya a wani lokaci daga nan sai a ɗauke tsawon sa'a huɗu ko biyar ba tare da an sake kawowa ba.

Kamfanin sarrafa lantarki na Nijar (Nigelec) ya ce matsalar na faruwa ne sakamakon katsewar lantarkin da ake samu daga Najeriya. Ƙasar dai wadda shugabanta Bola Tinubu ke jagorantar ƙungiyar Ecowas na ɗaukar wannan mataki ne a wani ɓangare na takunkuman da ƙungiyar ƙasashen ta Afirka ta Yamma ta ƙaƙaba wa Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.

Najeriya ita ce ƙasa mafi samar da lantarki ga Jamhuriyar Nijar.

Gwamnatin mulkin sojin Nijar dai ta sanar da buɗe kan iyakokin ƙasar da makwabtanta biyar, mako guda bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.

Manyan ƙasashen duniya da ƙungiyoyi da dama sun yi Allah wadai da juyin mulkin, sannan ana fargabar ɓarkewar rikice a yankin Sahel sakamakon juyin mulkin.

Cikin wata sanarwa da kakakin sojojin Kanal Manjo Amadu Abdurahamane ya karanta a gidan talbijin na ƙasar ya ce ''daga ranar 1 ga watan Agusta, an buɗe kan iyakokin ƙasar na tudu na ƙasashen Algeriya da Burkina Faso da Mali da Libya da kuma ƙasar Chadi''.

Sojojin sun sanar da rufe kan iyakokin ne a makon da ya gabata a daidai lokacin da suka sanar da kifar da gwamnati farar hula ta Mohamed Bazoum.

Kan iyakokin da aka sanar da buɗewan galibi na yankunan hamada ne masu nisa.

To sai dai har yanzu manyan hanyoyin hulɗar kasuwancin ƙasar na ci gaba a rufe sakamakon takunkumai da ƙungiyar Ecowas ta sanya wa ƙasar.

Juyin da sojoji suka gudanar a Jamhuriyar Nija,r shi ne na bakwai da aka samu cikin ƙasa da shekara uku a yankin yammacin Afirka, inda wasu ƙasashen da aka samu juyin mulkin suka dunƙule waje guda domin nuna adawa da sauran ƙasashen yankin 15.

Naɗa gwamnonin Jihohi

A cikin daren Talata ne kuma sojojin suka sanar da naɗa gwamnonin jihohin ƙasar bakwai.

Wakiliyar BBC da ke birnin Yamai ta ce matakin na nufin gwamnatin mulkin sojin sun sun kawo karshen mulkin gamnonin da suka yi aiki ƙarƙashin shugaba Bazoum.

Sanarwar sojojin ta ce sabbin gwamnonin jihohin ƙasar bakwai su ne:

  • Burgediya Janar Ibro Boulama a matsayin gwaman Agadez


  • Burgediya Janar Iro Oumarou, sabon gwamnan jihar Dosso


  • Burgediya Janar Ibrahim Bagadoma, jihar Diffa


  • Burgediya Janar Abdou Assoumane Harouna, sabon gwamnan Yamai


  • Manjo Kanal Oumarou Tawayé sabon gwamnan jihar Tahoua


  • Laftanar Kanal Maïna Boukar sabon gwamnan jihar Tillabery.


  • Kanal EF Labo Issoufou sabon gwamnan jihar Zinder


  • Sai babban kwantirolan 'yan sanda Issoufou Mamane a matsayin sabon gwamnan jihar Maradi


  • Kasashen Turai na ci gaba da kwashe mutanensu

    Wasu ƙasashen Turai suka fara kwashe mutanensu da ke Nijar, bayan da ƙasashen Mali da Burkina Faso, wadanda suma ke ƙarƙashin mulkin soji suka yi barazanar tayar Nijar din faɗa, idan Ecowas ta dauki matakin far mata da yaƙi.

    Tuni jiragen soji ɗauke da fararen hula mafi yawansu 'yan Faransa suka sauka a biranen Paris da Roma a ranar Laraba.

    Wani Bafaranshe da ke cikin mutanen da aka kwashe ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ''An shiga wani mummunan yanayi a Nijar, amma mun ji dadi tun da mun fito daga ƙasar mun dawo gida''.

    ''Muna fatan al'amura za su daidaita cikin kwanki ko makonni masu zuwa'', in ji shi.

    Manyan ƙasashen yamma irin su faransa da Amurka da Jamus da Italiya na da sojoji masu yawa a Nijar da ke yaƙi da 'yan ta'adda ko suke horar da dakarun ƙasar, ko taimaka wa sojojin kasar wajen yaƙar kungiyoyin masu iƙirarin jihadi irin su al Qaeda da ISIS.

    Kawo yanzu babu sanarwa daga waɗannan ƙasashe na janye dakarun nasu.

    Ministan tsaron Jamus ya ce babu wata damuwa game da tsaron sojojin Jamus da ke Nijar.

    Ministan harkokin wajen Italiya Antonio Tajani ya ce ƙasashen yamma ba za su ɗauki matakin soji don tilasta wa sojojin mayar da mulki ga farar hula, domin a cewarsa yin hakan ''tamkar sabon mulkin mallaka''.

    Nijar ce ƙasa ta bakwai mafi arzikizin ma'adinin Uranium a duniya, makamashin da ake amfani da shi wajen samar da makamashin Nukiliya da sinadarin magance cutar daji.

    A farkon makon da muke cikin ne hukumar tarayyar Turai ta ce tana da wadataccen makamashin na Uranium, domin kauce wa fargabar raguwar sidanarin da za a iya samu sakamakon rikicin juyin mulkin.

    Taron manyan hafsoshin tsaron Ecowas

    Manyan hafsoshin sojin ƙasashen yammacin Afirka za su yi taro a yau Laraba don tattauna batun juyin mulkin na Nijar.

    Taron wanda ke gudana a Abuja, babban birnin Najeriya, na daga cikin matsayar da aka cimma a taron da ƙungiyar Ecowas da gudanar a ƙarshen mako a Abuja, ƙarƙashin jagorancin shugabn Ecowa kuma shugaban Najeriya BVola Tinubu..

    A baya dai Ƙungiyar ta gargaɗi sojin da suka yi juyin mulkin su gaggauta mayar da mulki ga shugaba Mohamed Bazoum cikin mako ɗaya ko kuma su yi amfani da ƙarfin soji a kansu.

    Haka kuma ana sa ran wakilai daga ƙungiyar ta Ecowas za su isa birnin yamai domin fara tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkin ƙarkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani.