You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824791

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Neymar zai koma Al-Hilal ta Saudi Arabia daga PSG

Neymar Jnr Neymar Jnr

Paris St-Germain ta amince za ta sayar da ɗan kwallon Brazil, Neymar ga Al-Hilal ta Saudiyya kan fam miliyan 77.6 har da ƙarin tsarabe-tsarabe.

Kwantiragin ta dogara da idan an kammala auna koshin lafiyar ɗan wasan mai shekara 31, idan kuma ya samu takardar izinin shiga ƙasar.

Neymar wanda ya koma PSG kan Yuro miliyan 222 a 2017, bai buga wa PSG wasan Ligue 1 ba da Lorient ranar Asabar.

Ba ya cikin 'yan kwallon da sabon koci, Luis Enrique zai yi amfani da shi a bana a PSG.

Idan Neymar ya kammala komawa Al-Hilal, PSG za ta samu saukin biyan albashi mai ɗan karen tsoka, bayan da Lionel Messi ya koma Amurka a karshen kakar da ta wuce.

Ana hasashen cewar Neymar na karɓar albashin da ya kai fam miliyan 21.6 a duk shekara a kungiyar ta Faransa.

Ya buga wasa 173 a PSG da taimakawa kungiyar ta lashe kofi 13 ciki har da Ligue 1 biyar da zuwa wasan karshe a Champions League a 2020.

Sai dai ɗan kwallon tawagar Brazil, ya yi fama da jinya, hakan ya sa ba ya buga wasanni da yawa a PSG kamar yadda take bukata.

Likitoci sun yi wa tsohon ɗan kwallon Barcelona tiyata a cikin watan Maris, wanda daga lokacin ya kammala buga wasannin kakar da ta wuce.

Bai yi wa Brazil wasa biyu ba a gasar kofin duniya a 2022 a Qatar, bayan da ya ji rauni a wasan farko a wasannin.

Haka kuma Neymar bai yi wa Brazil Copa America ba a 2019, wanda ya ji rauni da wata jinyar da ya yi mai tsawo a 2021.