You are here: HomeAfricaBBC2023 02 07Article 1710035

BBC Hausa of Tuesday, 7 February 2023

Source: BBC

Neymar ya koma atisaye zai fuskaci Bayern Munich kenan

Neymar Jnr Neymar Jnr

Neymar ya koma atisaye a lokacin da Paris St Germain za ta buga wasa uku nan gaba masu mahimmaci.

Dan wasan tawagar Brazil, bai yi wa PSG karawa biyu ba - wasan Ligue 1 da ta doke Montpellier da kuma Toulouse – sakamakon jinya da ya yi.

Kenan dan kwallon yana da damar buga wa PSG wasan hamayya da za ta yi da Marseille ranar Laraba a karawar 'yan 16 a Coupe de France.

Haka kuma PSG wadda ke jan ragamar teburin Ligue 1 za ta kece raini da Monaco ta hudu a babbar gasar tamaula ta Faransa ranar Asabar.

Makon da za mu shiga PSG za ta kara da Bayern Munich a wasan farko na 'yan 16 a Champions League.

PSG ta saka hoton Neymar yana atisaye, yayin da shima Sergio Ramos ya warke yana karbar horo.

Sai dai Kylian Mbappe ba zai buga wasan hamayya da PSG za ta yi da kungiyar Jamus ba, sakamakon jinya da yake yi.

Kafin Neymar ya ji rauni, wanda ya yi bikin cikarsa shekara 31 da haihuwa ranar Lahadi ya ci kwallo 17 ya bayar da 14 aka zura a rawa a wasa 25 da ya yi a bana.

Kwallo 31 da Neymar ya yi sanadi a raga har da wadanda ya ci, ya yi kan-kan-kan da Kylian Mbappe, in banda Erling Haaland na Manchester da ke kan gaba a cin kwallaye a Turai mai 34 jimilla.