You are here: HomeAfricaBBC2023 07 20Article 1808792

BBC Hausa of Thursday, 20 July 2023

Source: BBC

New Zealand ta doke Norway a wasan farko

New Zealand mai masaukin baƙi ta buɗe gasar cin kofin duniya ta mata da nasara akan Norway New Zealand mai masaukin baƙi ta buɗe gasar cin kofin duniya ta mata da nasara akan Norway

New Zealand mai masaukin baƙi ta buɗe gasar cin kofin duniya ta mata ta Fifa ta 2023 a cikin salo mai ban sha'awa inda ta doke Norway 1-0 a wasanta na farko.

A wasan da aka buga a filin wasan Eden park da ke Aukland, Hannah Wilkinson ta ci kwallo daya mai ban haushi a minti 48 a gaban taron jama'a 42,137 da suka zo kallon wasan.

Duk da dai hankalin New Zealand ya so ya tashi a minti na 89, amma 'yar wasar Norway Ria Percival ta ɓarar da fenariti, bayan Tuva Hansen ta taba kwallo da hannu.

Magoya bayansu sun fito don taya 'yan wasansu murna da suka kasa samun nasara a wasanni 15 da suka buga a baya a gasar cin kofin duniya.

Norway, zakarun duniya a shekarar 1995, sun kusa rama kwallon da Wilkinson ta ci, amma Frida Maanum ta Arsenal ta zubar da wata babbar dama.

'Yan wasan New Zealand sun taka rawar gani kuma saura kadan da sun kara zura kwallo a raga amma golan Norway Aurora Mikalsen ta tare kwallon da Ali Riley ta buga.

An yi shiru na minti daya kafin a fara wasan don tunawa da wadanda suka mutu a wani mummunan hari da aka kai a Auckland da safiyar ranar Alhamis.