You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776848

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Neman lafiya na je ba gudun bincike na yi ba — Matawalle

Mohammed Bello Matawalle Mohammed Bello Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, Mohammed Bello Matawalle, ya ce ba gudun bincike ya yi ba neman lafiya yaje.

Cikin wata hira da BBC, gwamnan ya ce yanzu gashi ya dawo, kuma kowa ya san da cewa mutum zai iya kasancewa yau da lafiya gobe babu, don haka ya dan gamu da rashin lafiya ne shi ya sa ya fita kasar waje neman magani.

Ya ce, ‘’Alhamdulillahi na je na nemi magani kuma na samu sauki har ma gashi na dawo gida Najeriya, idan ma rade-radi ake cewa na gudu, to gashi na dawo kuma ina ma gidana har ma muna shirye-shiryen rantsar da sabon shugaban kasa.”

Gwamna Matawalle, ya ce ‘’ Duk wanda ke rade-radi a kaina wai na gudu saboda gudun bincike bayan na sauka daga mulki to dan kansa.”

Gwamnan na Zamfara ya ce batun EFCC na wai tana zarginsa da cin wasu kudade, wannan zargi ne kuma kotu ce kadai ke tabbatar da mai laifi da ma marar laifi inji shi.

Ya ce, ‘’ Tun da maganar zargi ce, ai sai a zuba ido aga mai kotu zata yi, don ni a shirye nake ga duk wanda ke tuhuma ta da aikata wani abu yazo gani.”

Gwamna Matawalle, ya ce batun mika mulki kuwa shi tuni ya mika nasa.

Ya ce, ‘’ Mun riga mun yi handing over.”

Gwamnan na Zamfara ya ce, babu abin da zai ce ga al’ummar Zamfara sai kara godiya garesu saboda hadin kan da suka bashi a tsawon mulkin da ya yi a shekara hudu.”

Ya ce, “ Ina kuma kara yi wa jihar Zamfara addu’a a kan Allah ya zaunar da jihar lafiya, kuma shi wanda zai hau mulkin, Allah ya bashi ikon yi wa kowa adalci, sannan ina kira ga al’ummar jihar su bashi hadin kai dan ya dace don jihar Zamfara ce a gaba da komai.”

“ Ina kara kira ga jama’ar jihar Zamfara da su ci gaba da yiwa sabon gwamna addu’a a kan Allah ya bashi ikon shawo kan matsalar da ke addabar al’umma ta tsaro, ni na yi iya kokarina Allah ya sani, don haka yanzu lokacinsa ne sai ya yi kokari ya samu damar kawo karshen wannan matsala.” Inji gwamna Matawalle.

Gwamnan na Zamfara Mohammed Bello Matawalle, ya dawo gida Najeriya ne a ranar Asabar 27 ga watan Mayun 2023, a yayin da ake tsakiyar rade-radin cewa ya gudu ya bar kasar don kaucewa bincike bayan saukarsa daga mulki.

Tun bayan faduwa zabe a zabukan gwamnonin jihohin kasar da aka yi a watan Maris ne aka daina ganinsa a bainar jama’a kuma daga bisani ta bayyana cewa ba ya kasar.