You are here: HomeAfricaBBC2023 03 28Article 1739522

BBC Hausa of Tuesday, 28 March 2023

Source: BBC

Namibia ta ci Kamaru ta koma ta daya a kan teburi

Tawagar Kamaru Tawagar Kamaru

Tawagar Namibia ta doke ta Kamaru da ci 2-1 a wasan neman shiga gasar kofin Afirka da suka buga ranar Talata.

Wasa ne na rukuni na uku da Namibia ta yi na biyu, ita kuma Kamaru ta buga na uku, domin shiga gasar kofin Afirka da za a buga a badi

Namibia ce ta fara cin kwallo bayan da suka koma zagaye na biyu ta hannun Peter Shalulile, sai Absalom Iimbondi ya kara na biyu saura minti 11 su tashi.

Daf da za a tashi daga karawar Kamru ta zare daya ta hannun Vincent Aboubakar.

Ranar Juma'a 24 ga watan Maris Namibia ta tashi 1-1 a gidan Kamru a wasan farko da suka kara a tsakaninsu a cikin rukuni.

Kawo yanzu Namibia ce ta daya a kan teburi na uku da maki biyar, sai Kamaru ta biyu mai maki hudu da Burundi ta karshe mai maki daya.

Tuni aka fitar da Kenya daga wasannin, wadda Fifa ta dakatar, bayan da gwamnatin kasar ke tsoma baki a fannin tamaula.

A cikin watan Yuni za su buga wasan karshe a cikin rukuni, inda Burundi za ta fafata da Namibia.