You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806416

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Najeriya ta cika alƙawarinta na kuɗin da take ba wa Tarayyar Afrika

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Najeriya ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na bayar da kasonta ga kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta hanyar ba da cikakken kudin gudummuwarta na shekarar 2023 baki daya.

Babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen kasar, Ambasada Adamu Ibrahim Lamuwa, ne ya tabbatar da hakan a gefen taron majalisar zartarwa ta AU karo na 43 a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Ambasada Lamuwa ya yi maraba da yadda aka yi la'akari da yanayin tattalin arzikin kasashen Afirka a halin da ake ciki, wajen tsara kasafin kudin kungiyar da kuma yadda kowa ce kasa za ta bayar da gudummarwata.

Ya kuma jaddada bukatar bin ka'idojin bincike kan kudin da ake kashewa a kungiyar don tabbatar da gaskiya da rikon amana.

An tsara Shugaba Tinubu zai halarci taron shirya manufofi na kungiyar na tsakiyar shekara karo na 5 ranar Lahadi a birnin Nairobi, inda za a tattauna kan wasu muhimman batutuwa.

Ambasada Lamuwa ya kuma bayyana cewa an yi wa taron na matakin ministoci da ya gudana gabanin halartar shugabannin kasashen AU taken ilimi a kasashen AU a shekarar 2024.

Najeriya na daya daga cikin manyan kasashen da suka fi bayar da gudummawar kudi ga kungiyar ta Tarayyar Afirka (AU).

Kasafin kudin AU na shekarar nan ta 2023 na dala miliyan 654.8 ana gudanar da shi ne ta hanyar gudunmawar doka ta shekara da gudummawar sa-kai daga abokan hulda, da kuma sauran kudaden shiga daban-daban.