You are here: HomeAfricaBBC2021 06 07Article 1280605

BBC Hausa of Monday, 7 June 2021

Source: BBC

'Na shiga mummunan yanayi lokacin da na ga gawar ɗa na'

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Mahaifin daya daga cikin samarin nan sama da 10 na jihar Kano da sukai hatsarin mota a kan hanyar dawowa daga jihar Kaduna daurin aure, ya shaidawa BBC cewa ya samu kan shi cikin tashin hankali lokacin da aka fada masa mutuwar Dan shi.

Ahmad Dahiru Beli, mahaifin daya daga cikin matasan mai suna Abba Ahmad ya ce a lokacin da aka kira kan cewa yaran sun yi hatsarin mota, an kuma samu hasarar rayuka wadanda suka shaida ma sa sun yi kokarin sakayawa ba tare da sun tabbatar da Dan shi na daga cikin wadanda suka rasu ba.

''Tun lokacin da suka fara shirin tafiyua, motar farko ta cika sai ya shiga ta biyu akan ido na. Dimautar da na shiga ba ta misaltuwa, ko da aka kira kan cewa an samu wadanda suka rasu ba su fadi sunan kowa ba.

Na shiga dimuwa da tashin hankali a lokacin da na ga gawar shi ba, zuciyata ta fada min ba zan iya kallon yanayin ba na je na duba na tabbatar da cewa tabbas Dana na ciki, daman tun da farko da aka sanar da batun hatsarin na fawwalawa Allah ina ta ambaton Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.

Da farko mahaifiyarsa ba ta nuna damuwa sosai ba amma bayan zuwan dangi da 'yan uwanta suka samu labarin yadda lamarin ya faru sai suka raunana mata zuciya suka fara koke-koke, amma daga bisani an shawo kan lamarin, mu na da kyakkyawan fatan sun yi kyakkyawan karshe,'' inji malam Ahmad.

Baya ga matasan na jihar Kano su 9 da hatsarin motar ya rutsa da su, akwai kuma wasu biyar da ke cikin karamar motar da sukai taho mu gama, wanda su ma nan ta ke Allah ya dauki rayuwarsu.

A bangare guda, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ya daku da labarin mutuwar matasan 'yan asalin Jihar Kano da hatsarin motar ya rutsa da su ranar Asabar akan hanyar su ta Kano zuwa Zaria.

Cikin wata sanarwa da mai magana yawun gwamnan Abba Anwar ya fita ta ce "Mutuwarsu ta yi matukar girgiza mu."

"Wannan babban rashi ne ba kawai ga iyalai da kuma 'yan uwansu ba har ma ga gwamnati da kuma al'ummar jihar kano baki daya," ta kara da cewa.

Ana yawan samun hadarin mota da ke janyo asarar rayuka da dukiyar jama'a a titunan Najeriya, musamman babban titin Kano zuwa Abuja wanda ake aikin gyaran shi. A bangare guda kuma wasu na dora alhakin yawan hatsarin motar ko dai kan rashin kaywu da ingancin titunan ko kuma tsananin gudun da direbobi ke yi.