You are here: HomeAfricaBBC2023 09 14Article 1844357

BBC Hausa of Thursday, 14 September 2023

Source: BBC

Na san yadda zan yi da masu yi mani ihu - Maguire

Harry Maguire Harry Maguire

Ɗan wasan baya na Ingila Harry Maguire ya ce abin da magoya baya suka yi masa a wasansu da Scotland "raha ce kawai" kuma ya san "yadda zai ji da lamarin".

Magoya bayan Scotland sun dinga tsokanar ɗan bayan na Manchester United ranar Talata a wasan sada zumunta da suka yi, inda suka dinga taɓa masa duk lokacin da ya ba da fasin.

A ƙarshe dai har zuwa lokacin da ɗan ƙwallon ya ci gidansu a wasan da Ingila ta yi nasara da ci 3-1.

"Lamarin ya ɗauke duk wata damuwa daga kan sauran abokan wasana kuma ya dawo kaina gaba ɗaya," in ji Maguire.

"Tabbas hakan ya sa sun murza leda da kyau."

Kocin Ingila Gareth Southgate ya yi tir da "halayyar maras kyau" da ake nuna wa Maguire bayan wasan, yana mai cewa sukar da ɗan wasan ke sha "raha ce kawai".

Mahaifiyar Maguire ta ce cin zarafin ɗanta da ake yi ya wuce maganar ƙwallon ƙafa kawai.

Maguire na fuskantar suka a kafofin yaɗa labarai da kuma dandalin sada zumunta, abin da ya kai ga magioya bayan ƙungiyoyinsa yi masa ihu a tawagar Ingila da Man United.