You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218178

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

NPFL: Kano Pillars ta zama ta biyu bayan ta doke Heartland

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta doke Heartland ta garin Owerri 2-1 a wasan mako na 18 na gasar Firimiyar Najeriya.

Sakamakon ya bai wa Masu Gida damar hawa mataki na biyu da maki 33, daidai da Kwara United ta saman teburi.

Chidera Eze na Heartland ne ya fara zira wa Pillars ƙwallo a raga a minti na 39 kafin daga bisani Rabiu Ali ya farke ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.

Ana cikin minti na 9 da aka ƙara a kan 90 ne kuma Ebuka David ya ƙara ta biyu daga bugun finareti.

Wasan wanda aka buga a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna wato gidan Kano Pillars, ya zama na 10 da ta yi nasara cikin 18 da ta buga a kakar bana ta 2020/2021.

Sauran wasannin da aka buga ranar Lahadi:

Akwa Utd 3-0 Lobi

Rivers Utd 1-0 Sunshine Stars

Plateau Utd 2-1 Rangers

Nasarawa Utd 5-3 Abia Warriors

Katsina Utd 1-2 Kwara Utd

Adamawa Utd 0-0 Wikki

Kano Pillars 2-1 Heartland

Wolves 3-1 FC Ifeanyi Ubah

Join our Newsletter