You are here: HomeAfricaBBC2023 06 06Article 1781348

BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

NLC da TUC sun fasa shiga yajin aiki kan cire tallafin fetur a Najeriya

Hoton alama Hoton alama

Manyan kungiyoyin kwadago biyu a Najeriya, NLC da TUC sun jingine aniyarsu ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani wanda suka shirya farawa ranar Laraba kan tashin farashin man fetur.

Kungiyoyin biyu sun yanke wannan shawarar ce bayan ganawar da suka yi da bangaren gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa, ranar Litinin.

A makon da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadago na Najeriya suka bai wa gwamnatin kasar wa’adin zuwa ranar Talata 6 ga watan Mayu domin ta janye cire tallafin man fetur ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da matsayar, wadda shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Joe Ajero ya tabbatar, bayan kwashe kimanin sa’a shida ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

Wata sanarwar da shugabannin NLC da TUC suka sanyawa hannu, ta ce daya daga cikin dalilan jingine yajin aikin shi ne bai wa gwamnatin tarayya da bangaren ‘yan kwadago damar kafa wani kwamiti da zai duba batun yin karin albashin ma’aikata da kuma lokacin da za a aiwatar da tsarin.

Haka nan kuma za a duba tsarin bayar da tallafin kudade na Bankin Duniya ta yadda za a sanya masu karanin karfi a ciki.

Daga nan kungiyar kwadagon da gwamnati za su sake duba tsarin gyaran matatun man fetur na kasar ta yadda za a iya kammala gyara su.

Bugu da kari gwamnati za ta samar da tsarin gyara hanyoyin mota da kuma samar da layukan dogo a fadin kasar.

A karshe sanarwar ta ce kungiyar kwadago za ta sake yin wani zama da gwamnatin tarayya a ranar 19 ga watan Yuni domin samar da matsaya kan yadda za a aiwatar da tsare-tsaren da aka cimma.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne dai ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin jawabinsa na karbar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Wani lamari da ya jefa bangaren man na Najeriya cikin hali na rashin tabbas.

Farashin litar man fetur ya yi tashin gwauron zabi zuwa sama da naira 500 daga kimanin naira 200 da yake a baya.

Kungiyar kwadago dai ta dage kai da fata cewar ba za a cire tallafin man fetur din ba har sai an yi tanadin abubuwan da za su kawo sauki ga al’ummar kasar.

Yayin da farashin man fetur din ya nunka kusan sau biyu bayan cire tallafin, mafi karancin albashin ma’aikatan gwamnati na nan a naira 30,000.

Tashin farashin man fetur a Najeriya dai na nufin tashin farashin sufuri da na abinci da ma na dukkanin kayan masarufi, wani lamari da ake ganin zai kara jefa al’ummar kasar cikin wahala.