You are here: HomeAfricaBBC2022 10 20Article 1646837

BBC Hausa of Thursday, 20 October 2022

Source: BBC

Na san yadda zan yi da Ronaldo da ya fice daga filin wasa kan a tashi - Ten Hag

Ronaldo da kocin Man United Ten Hag Ronaldo da kocin Man United Ten Hag

Dan wasan Manchester United na gaba Cristiano Ronaldo ya fice dafa filim wasana Old Trafford kafin tashi daga wasan da kungiyar ta buga da Tottenham a ranar Laraba. Ba a yi amfani da Ronaldo ba wanda aka ajiye a benci a wasan da United ta yi nasara da ci 2-0, dan wasan ya shige dakin sauya kaya ne tun ana minti na 89. Ko wa ya ga shigar dan wasan cikin sauri cikin dakin sauya kaya, gabanin tashi daga wasan kuma a fusace. Baya kammala wasan kocin kungiyar Erik ten Hag ya ce "zai ji da lamarin" a ranar Alhamis. "Na ga fitar shi, amma ban ce masa kala ba," in ji Ten Hag. Canji uku kawai United ta yi cikin biyar da take da shi lokacin da Ronaldo ya ta shi daga benci, jim kadan bayan Ten Hag ya sanya Christian Eriksen da Anthony Elanga. Ronaldo ya nuna rashin jin dadinsa a fili bayan sauya shi da aka yi a wasan da kungiyar ta buga a ranar Lahadi a wasan da ta tashi 0-0 da Newcastle. Jim kadan bayan kammala wasan Ten Hag ya ce ba shi da "matsala" da matakin Ronaldo amma dole za a fahimtar da dan wasan ya tsaya. Tsohon dan wasan Ingila Gary Lineker ya ce fitar Ronaldo ta ja hankalin masu kallon wasan duk da cewa United ta yi abin da ya kamata a wasan. "Abu ne da za a a yarda da shi ba - kwata-kwata bai da ce ba," in ji Lineker.