You are here: HomeAfricaBBC2023 02 23Article 1720079

BBC Hausa of Thursday, 23 February 2023

Source: BBC

Mutane da dama sun jikkata a rikicin siyasar Kano

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Bayan wani ɗauki ba daɗi da aka yi a yayin taro ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Injiniya Rabi'u Musa kwankwaso a jihar Kano.

Yanzu a iya cewa ƙura ta lafa somin kuwa an samu ɗaukin jam'an tsaro waɗanda suka tabbatar da komai ya koma daidai.

Rahotanni sun bayyana cewa dandazon magoya bayan Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ne suka yi dafifi domin tarbarsa tun daga Kwanar Dangora, wanda hakan ya janyo tashin hankalin da ya yi sandin jikkatar mutane da dama.

Magoya bayan jam'iyyar ta NNPP sun zargi "ɓangaren gwamnatin jihar Kano da sanya 'yan banga su afka musu", amma gwamnatin jihar ta musanta wannan zargi tana cewa "ba haka lamarin yake ba".

Waɗanda suka shaida faruwar lamarin sun faɗawa BBC cewa hargitsin ya kaure ne tsakanin ɗaruruwan magoya bayan Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da wasu da suke zargin magoya bayan APC ne, yayin da suke kan hanyarsu ta shiga birnin Kano.

"da muna tahowa mun samu motocin da aka farfasawa gilasai, am raunata mutane haka, bayan mun wuce munga 'yan daba da suka taru a wajen gadar Na'ibawa.

"Na ga mutane da dama sun jikkata amma tun da ba tsayawa na yi na ƙirga ba, ba zan iya cewa ga adadinsuba," in ji wani mutum da BBC ta tattauna da shi.

Wani da aka fasawa mota a dai-dai Na’ibawa ‘Yan Lemo, yace wasu mutane ne suka yi shaga irinta Kwankwasawa da jar hula da riga, suka auka musu.

"Wani maimota ne ya riƙa binmu a jiki yana danna mana hon cewa mu kauce, ko da na taka birki sai naga ashe matasa ne da makamai a motarsa suka fito suka auka mana.

"An ƙona mana mota Corolla LE da Vibe guda, jami'an tsaro sun zo, sojoji sun yi ƙoƙari sun riƙa bin mutane suna kamawa," in wani shi ma da abin ya rutsa da shi.

Jam’iyyar NNPP dai ta zargi wasu da ƙoƙarin hana Injiniya Rabiuu Musa Kwankwaso zuwa Kano ya ƙada kuri’arsa a matsayinsa na dantakarar shugaban ƙasa.

Alhaji Umar Haruna Doguwa shi ne shugaban jam’iyyar yace sun yi niyar suyi gangamin yaƙin neman zaɓe a yau amma suka janye.

"Shi ɗan takara ne, yana da damar zuwa gida mahaifarsa ya kaɗa kuri'arsa a ranar zaɓe, bai kamata a yi ƙoƙarin hana shi ba," in ji Doguwa.

BBC ta tuntuɓi jam'iyyar APC da aka zarga kan wannan batu, Alhaji Garba Yusuf Abubakar mamba ne a kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna na jam’iyyar APC kuma kwamishinan ruwa na jihar Kano, ya ce ba haka lamarin ya ke ba.

"Wata uku mun fitar da jadawalinmu na yaƙin neman zaɓe, sai muka ji labarin sun fito, duk da haka kuma an hana mu fita kuma ba mu fita ba, kaga ai babu maganar a zarge mu cikin wannan lamari".

Sai dai ɗazu kakakin rundunar 'yan sandan jihgar Kano SP Haruna Kiyawa ya ce kwamishinan 'yan sanda ya gayyaci shugabannin jam’iyyu na jihar don yin ganawar gaggawa da su kan wannan lamari.