You are here: HomeAfricaBBC2023 07 28Article 1814186

BBC Hausa of Friday, 28 July 2023

Source: BBC

Munich za ta sake taya Kane, Fulham ta taya Callum Hudson-Odoi

Harry Kane Harry Kane

Shugabannin Bayern Munich sun tafi London don sake sabuwar tattaunawa da Tottenham a kan yarjejeniyar fam miliyan 86 da za a yi a kan dan gaban Ingila Harry Kane. (Telegraph - subscription required)

Paris St-Germain ta yi amanna cewa zata daukar Kane muddin Tottenham ta zabi ta sayar da shi. (Sky Sports)

Manchester United na ci gaba da tattaunawa da Fiorentina a kan dan tsakiyar Morocco Sofyan Amrabat,mai shekara 26, yayin da kuma suke kokarin cire dan wasan Brazil Fred daga cikin kungiyar. (90min)

Chelsea ta fuskanci damuwa a kokarinta na daukar dan wasan Argentina Paulo Dybala da ya sake sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da Roma. (Tuttomercatoweb - in Italian)

Bayern na sha’awar mai tsaron ragar Brentford dan kasar Spaniya David Raya, mai shekara 27, da kuma David de Gea wanda bashi da kungiyar da zai bug awa wasa bayan ya bar Manchester United. (Times - subscription required)

Shi kuwa dan tsakiyar Italiya Marco Verratti, mai shekara 30, ya kusa kamala yarjejeniyar komawa Al Hilal daga Paris St-Germain. (Fabrizio Romano)

Dan tsakiyar Ajaz dan kasar Ghana, Mohammed Kudus, mai shekara 22, ya fi nuna sha’awarsa ta koma wa Arsenal a kan Chelsea. (Football Transfers)

Chelsea ta yi tayin dan wasan Faransa na kungiyar Montpellier Elye Wahi a kan fam miliyan 24, abin da aka ki amincewa da shi. (Standard)

Chelsea na duba yiwuwar daukar dan wasan Southanmpton dan kasar Belgium Romeo Lavia, bayan da aka ki amincewa da tayin da ta yi a kan dan wasan Brighton Moises Caicedo a kan fam miliyan 80. (Athletic - subscription required)

Fulham ta taya dan gefen Chelsea Callum Hudson-Odoi, mai shekara 22, a kan fam miliyan hudu. (Fabrizio Romano)

Tsohon dan tsakiyar Everton James Rodriguez na dab da komawa Sao Paulo kungiyarsa ta goma da zarar kwantiraginsa ta kare da inda ya bugawa wasa. . (Sun)

Shi kuwa tsohon dan tsakiyar Aston Villa, Arjan Raikhy, mai shekara 20, ya kusa kamala yarjejeniya da Leicester City. (Sky Sports)