You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837742

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

Source: BBC

Muna ji a jikinmu bayan cire tallafin man fetur - ‘Yan Najeriya

Hoton alama Hoton alama

A Najeriya, janye tallafin man fetur na cikin manyan matakan da gwamnati Bola Ahmed Tinubu ta fara dauka da nufin magance matsalar karancin mai da cuwa-cuwa ko cin hancin da ake zargin yana tattare da harkar mai.

Sai dai janye tallafin ya jefa ‘yan kasar da dama a cikin mawuyacin hali, sakamakon hauhawar farashin kayan masarufi.

Mahukunta na ikirarin daukar matakai da nufin rage radadin janye tallafin, amma ganin da sannu yanzu ana maganar cikar sabuwar gwamnatin kwana dari, wasu ‘yan kasar sun fara yanke kauna game da batun samun sauki, sakamakon yadda tsadar rayuwa ke karuwa.

‘’Gaskiya tsadar rayuwa ta yi wa ‘yan Najeriya yawa. Farashin kayan masarufi ya karu, yana ta ninninkawa.’’ in ji wani mai sana’ar sayar da lemo.

Kuma irin kalaman da ke fitowa daga bakunan mafi yawan ‘yan Najeriya ke nan da ke nuna cewa rayuwarsu ta gigita, suna fama da matsai da tsanananin tsadar rayuwa, sakamakon janye tallafin mai da sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya sanar a karshen watan Mayun wannan shekarar, wato lokacin da ya sha rantsuwa ta karbar ragamar mulki.

'Kasuwa ta yi halinta'

A baya, farashin litar man fetur bai wuce naira dari da sittin da biyar ba a farsahin gwamnati, a lokacin zuwanta, sai dai yanzu ya nausa zuwa naira dari shida da doriya; kasancewar gwamnati ta kakkabe hannunta ta bari kasuwa ta yi halinta.

Wannan ne ya yi sanadin hauhawar farashin kayan masarufi da sauran abubuwan more rayuwa.

Har ta kai ga wasu daga cikin farashinsu ya yi tashin gwauron-zabi, ya ninninka!

Mai sana’ar lemon, wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce bai taba shiga irin wannan matsin ba!

"Buhun lemo yanzu ana sayar da shi naira dubu goma sha biyar zuwa dubu goma sha shida ban da kudin mota.

Kuma bayan ka kasa lemon ma ba a ciniki, saboda babu kudin saye a hannun jama'a.

Ka san lemo ba a sayen sa sai an ci an koshi. Kuma ka ga ana fama da yunwa. Muna fama da matsin rayuwa. Ga shi ni a wannan yanayin ma matata ta haifa mana tagwaye."

Sana’armu na gab da durkushewa saboda cire tallafin man fetur - Direbobi

Bangaren sufuri, musamman na masu motocin haya, na cikin sassan da janye tallafin ya ji musu sosai.

Binciken da BBC ta yi a tashar motar Karu da ke babban birnin tarayya ya nuna cewa akwai tarin motocin safa jibge saboda rashin fasinja.

Mallam Jibrin Aliyu shi ne shugaban reshen Karu na kungiyar dirobobi ta kasa, wanda ya ce idan ba a samu mafita ba, sana`arsu na gab da durkushewa.

“A baya mukan loda mota sama da goma da ke zuwa jiha daya daga cikin jihohi daban-daban na Najeriya a rana daya. Yanzu da kyar muke loda mota daya saboda babu fasinja.

Rayuwar ta tsananta. Mutane da dama sun gwammace su tura sako maimakon su yi bulaguro. Saboda haka sai ka ga mota ta yi kwana ashirin tana layin jiran lodi. Muna matukar jin jiki.’’

Rayuwar Makanikai ta dogara ne jikin masu mota. Kuma wannan janye tallafin ya sa suna gani a kwaryar shan su!

Malam Ahmad Shuaibu wanda ke aikin Ruwaya ko latirisha ya ce adadin masu hawa mota ya ragu sosai don haka lallaba rayuwar suke yi. Sukan wuni ba wani aikin a zo a gani sai dai hamdala.

‘Gwamnati ba ta jin shawara’

Mahukunta a Najeriyar dai na daukar matakai daban-daban da nufin rage radadin janye tallafin, ciki har tallafin kayan abinci da takin zamani. Amma rahotanni na nuna cewa kayan agajin tamkar a jefa digon ruwa ne a cikin teku. Domin haka tasirinsa ragagge ne.

Kodayake Masana sun shawarci gwamnati, dangane da irin matakan da ya kamata a dauka, kafin janye tallafin. Sai dai a cewar, Dr Ahmed Adamu, masanin tattalain arzikin man fetur, ba daya daga cikin dimbin shawarwarin da za a ce gwamnati ta yi aiki da shi.

“Muhimmai daga cikin shawarwarin da muka bayar su ne a inganta tattalin arziki ta yadda mutane za su samu kudi a hannu su sayi abubuwan biyan bukata ba tare da sun ji radadin janye tallafin ba. Shi ya sa muka ce a kashe kudi a kan harkar sufuri, sannan a samar da matatun mai da makamashi musamman iskar gasa. Kuma har yanzu ba a yi hakan ba.”

Gwamnatin Najeriyar dai na cewa wannan matsin rayuwa na wani lokaci ne, don haka bayan wuya sai dadi.

Amma ganin matsin sai kara tsananta yake yi a daidai lokacin da ake maganar cika kwana dari ta gwamnatin shugaba Tinubu, wasu ‘yan kasar na cewa sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.