You are here: HomeAfricaBBC2023 05 25Article 1773896

BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023

Source: BBC

Mun ci gajiyar rufe boda – Ƙungiyar manoman Najeriya

Hoton alama Hoton alama

Yayin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke ƙoƙarin miƙa mulki bayan shekara takwas, shin wane tasiri manufofinta suka yi kan harkar noma?

BBC ta tattauna da shugabannin wasu ƙungiyoyin manoma a Najeriyar waɗanda suka bayyana yadda harkar noma ta kasance a tsawon mulkin shugaban mai barin gado.

Akasarin manoman sun yaba wa gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari, waɗanda suka ce harkar noma ta inganta ta hanyar taimaka masu tsayawa da ƙafafunsu.

Manoman sun ce a cikin shekara takwas na gwamnatin Muhammadu Buhari, shugaban ya ɓullo da shirye-shirye wadanda suka amfanar da su tare da samar da wadataccen abinci da ake amfani da shi a ƙasar.

Ɗaya daga cikin matakan da Buhari ya ɗauka shi ne garƙame iyakokin ƙasar ta ƙasa inda aka hana shiga da shinkafa yar waje cikin Najeriya.

Shugaban ƙungiyar manoma ta NICAS, Sadiq Daware ya ce manoma sun ci gajiyar gwamnati da za ta tafi.

"Rufe bodojin da Muhammadu Buhari ya yi, shi ne da kyakkyawar niyya kuma ya taimaka wa ƙasa ƙwarai da gaske.

"Akwai (tsari) da aka kawo da Turancin Ingilishi, 'Presidential Fertilizer Initiative' saboda sawwaƙa wa manoma harkar taki da kuma bai wa ƙananun manoma rance da kuma wani shiri domin tallafa wa kamfanonin masu shinkafa."

A cewarsa, sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar manoman Najeriya ta AFAN, Hon. Muhammad Magaji, ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta ciri tuta a harkar noma.

"Manomanmu suna iya ciyar da kansu daidai gwargwado ba kamar irin yadda aka yi a baya ba, musamman lokacin da aka shiga covid-19.

"Ba dan Allah ya qaddara cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi hangen nesa, wato an fito da tsare-tsaren noma, da ba haka ba."

Wasu ƙarin manoman sun ce gwamnatin Buhari ta amfane su kuma ta taimaka musu.

"A gwamnatin Buhari, ya ba mu kamar su taki, kamar injin feshi har da kuɗi ma an bamu domin a gwamnatinsa ne manomi ya san lalle ashe arziki yana noma."

Ya bayyana cewa a jihar Kebbi, harkar noma - musaman noman rani na shinkafa da alkama, ta ciri tuta saboda ta taimaka wajen samar wa matasa aikin yi.

Shugaban manoman, Hon. Muhammad Magaji da kuma Sadiq Daware sun fadi wasu daga cikin buƙatun `yanuwan nasu.

"Manomi yana so a sama masa taki a lokacin da ya kamata, ana gama aikin gona, a sama masa kasuwa ta gaskiya."

Ya ƙara da cewa "Kasan nan muddin muna son a sami ci gaba, muna son a inganta sana`oi, ana so kuma a samarwa da mutane aikin yi, toh dole a mai da hankali a wajen noma."

Shugaba Buhari ya sha cewa babu shakka a yanzu manoma a Najeriya na iya ciyar da ƙasar ba sai an jira abin da ƙasashen ƙetare suka girba ba.

Gwamnatin Buharin za ta sauka nan da 29 ga watan Mayu, kuma ita ma sabuwar da za ta shigo tana da nata manufofin kan noma da kiwo a yayin da suma manoman na da na su buƙatun.