You are here: HomeAfricaBBC2023 12 13Article 1898120

BBC Hausa of Wednesday, 13 December 2023

Source: BBC

Mummunan ƙarshe da Manchester United ta yi a tarihin Champions League

Yan wasan Manchester United a jimami Yan wasan Manchester United a jimami

Dawowar Manchester United Champions League wani ɓangare ne na ƙoƙarin gyaran da ake neman kawowa a United wanda ya janyo aka kawo Erik ten Hag a matsayin wanda zai sauya ƙungiyar daga cin kashin da take fuskanta a filin wasanta na Old Trafford da a baya ya zama abin tsoro.

Ana ta farin ciki cewa United ta dawo kan ƙadaminta na zuwa Gasar Zakarun Turai, bayan dogon lokacin da aka shafe tana shan wuya a hannun masu horaswa da dama kamar Louis van Gaal da Jose Mourinho - ko da yake ya ci League Cup da Europa League – sai kuma ɗan lelen da aka yi wa uzuri, Ole Gunnar Solskjaer.

Ten Hag ya yi nasara wajen lashe League Cup a kakarsa ta farko, amma ƙasƙancin da Manchester United ke fuskanta da kocinta, na neman durƙusar da yunkurin sauyin da ake son kawo wa a ƙungiyar.

Wannan shekara ce mai cike da rudani, Manchester United ta ƙare a ƙarshen teburi a gasar Zakarun Turai a rukunin da Bayern Munich ta yi ta farko FC Copenhagen ta yi biyu sai kuma Galatasaray ta yi ta uku.

Filin Champions League wuri ne da ko me ya faru ba a mantawa da shi ba kuma a yafewa. Duk wani magoyin bayan United yana da tabbas tun da fari ba za su yi wani abun azo a gani ba.

Yanzu dai ta ƙare ba tare da kyakkyawan ƙarshe ba, United ba ta da wani kofin Turai da take bugawa bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Bayern 1-0, a wasan har aka tashi ba ta kai harin zuwa raga ba.

A tarihin Champions ba a taɓa cin wata kungiya kwallo mai yawa ba a rukuni kamar yadda aka zuba wa Onana har kwallo 15.

An fuskanci yanayin hawaye a Old Trafford lokacin da magoya baya suka zauna a kujerunsu kamar wadanda aka liƙe har sai da suka ji busar karshen lokaci daga alƙalin wasa ya tashi wasan.

Dubban magoya bayan United sun yanke ƙauna tun ana tsaka da wasan, sai dai babban tambaya ita ce wa yakamata a zarga game da rashin ƙoƙarin United?

Tsugune ba ta ƙare ba

Da yawa na ganin ba a nan matsalar da Man U ke ciki za ta ƙare ba, ganin wasannin da ke gabanta musamman a wannan watan na Disamba.

A ranar Lahadi za ta je Anfield gidan Liverpool inda ta kwashi kashinta a hannu da ci 7-0 a watan Maris.

Daga nan kuma za ta garzaya West Ham, sai ta koma gida inda Aston Villa da ke matsayi na uku a Premeir za ta ziyarce ta.