You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776800

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Muhimman alƙawuran da Tinubu ya ɗauka

Shugaba Bola Tinubu Shugaba Bola Tinubu

Daga Litinin, 29 ga watan Mayu, ba za mu sake jin "zaɓaɓɓen shugaba" ba ko "shugaba mai jiran gado" idan ana maganar Bola Ahmed Tinubu.

Idan kuma ana maganar Muhammadu Buhari ne, ba za mu sake jin "Shugaba Buhari" ba ba tare da kalmar "tsoho" ta zo a farko ba.

Hakan ta faru ne sakamakon rantsuwar kama aiki da sabon shugaban na Najeriya ya sha a dandalin taro na 'Eagle Square' da ke birnin Abuja a matsayin shugaban Najeriya na 16.

Shugabannin ƙasashen duniya kimanin 24 ne suka halarci bikin, kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC Hausa.

Kazalika ƙasashen Amurka da Birtaniya sun tura tawagogi na wakilci.

Jawabin da Tinubu ya gudanar cike yake da ƙarfafa gwiwar ƴan Najeriya, da neman haɗin kan ƙasa.

Sai dai wasu daga cikin alƙawuran da ya ɗauka sun shafi sake fasalin matakan da gwamnatin Buhari ta ɗauka a fannin tattalin arziki.

Tun kafin kammala taron tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da matarsa Aisha suka kama hanyar zuwa Daura, inda suka isa a tsakiyar ranar ta Litinin.

Mun duba mafiya muhimmanci daga cikin alƙawuran da ya ɗauka a jawabin nasa.

'Zan sake duba maganar sauya fasalin kuɗi'

Wasu ba za su yi mamaki ba game da alwashin da Tinubu ya ci na sake duba batun sauya fasalin kuɗi na naira, ganin cewa tun kafin ya ci zaɓe yake sukar lamarin.

Haka nan, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sababbin takardun nairar da aka sauya. Sai dai bai faɗi har zuwa yaushe ba.

"...Tsarin sauya fasalin kuɗi da CBN ya gabatar ya yi wa mutane tsauri, ganin irin yawan 'yan Najeriyar da ba su da asusun banki," in ji Tinubu.

"A gefe guda kuma, gwamnatina za ta ci gaba da amfani da dukkan kuɗaɗen a matsayin abubuwan cinikayya."

Kazalika, ya ce kuɗin ruwan da CBN ya ƙara ya yi yawa, kuma "akwai buƙatar a rage shi don ƙara yawan zuba jari da kuma haɓaka cinikayya waɗanda za su tallafa wa tattalin arziki gaba ɗaya".

Daidaita darajar naira

Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙuntata wa rayuwar 'yan Najeriya shi ne faɗuwar darajar naira, wadda ke da farashi iri-iri hatta a wajen Babban Bankin Ƙasa CBN.

Tinubu ya yi alƙawarin bin hanyoyin daidaita darajar tata.

"Tsare-tsaren kuɗi abu ne da ke buƙatar kyakkyawan tunani. Wajibi ne CBN ya samar da farashin canji bai ɗaya. Hakan zai sa a daina saye da sayar da kadarori cikin sauri kuma a koma zuba jari da samar da ayyukan da za su taimaka wa tattalin arziki a aikace."

Tallafin man fetur ya ƙare

Sabon shugaban ya ce daga yanzu gwamnatinsa za ta soke batun bayar da tallafin man fetur a Najeriya, saboda dama bai gaji tanadin kuɗin ba a kasafin kuɗi na 2023.

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta karkata kuɗaɗen zuwa wasu ɓangarorin ci gaban ƙasa.

"Tallafin man fetur ya tafi," in ji shi. "Muna yaba wa tsohuwar gwamnati bisa ƙoƙarin janye tallafin man fetur a hankali, wanda yake ƙara wa mai ƙarfi ƙarfi fiye da talaka."

Ya ƙara da cewa: "Ba zai yiwu tallafin ya ci gaba da laƙume kuɗaɗe ba yayin da muke ƙarancin kuɗi. A madadin haka, za mu mayar da kuɗin wajen ayyukan raya ƙasa, da ilimi, da harkokin lafiya, da kuma ayyukan da za su kyautata rayuwar miliyoyin 'yan ƙasa."

Samar da aikin yi miliyan ɗaya a ɓangaren fasahar zamani

Shugaban ya kuma yi bayani kan harkar fasahar zamani, wadda matasa ne suka fi cin gajiyarta.

A cewarsa "Gwamnatina za ta ƙirƙiri damarmaki ga matasa. Za mu martaba ƙudurin da muka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe nacewa za mu samar da guraben ayyuka miliyan ɗaya a ɓangaren fasahar zamani."

"Za mu haɗa hannu da Majalisar Dokokin Tarayya wajen samar da dokar samar da ayyuka. Dokar za ta sakar wa gwamnati mara wajen inganta hanyoyin samar da aikin yi..."

'Tsaro ne zai zama babban jigo a gwamnatinmu'

Kamar yadda Buhari ya sha nanatawa, shi ma Tinubu ya ce magance matsalar tsaro zai saka a gaba tsawon shekara huɗu masu zuwa.

A cewarsa "Tsaro ne zai zama babban ƙudirin wannan gwamnatin, saboda ba za a samu adalci ba ko ci gaba matuƙar akwai rashin tsaro da tashin hankali," kamar yadda ya bayyana.

"Don daƙile wannan bala'i, dole ne mu gyara tsarin tsaronmu da ma fasalinsa. Za mu ware ƙarin kuɗi ga jami'an tsaronmu, ba wai yawansu kawai za mu ƙara ba.

"Za mu ba su ƙarin horo, da kayan aiki, da ƙarin albashi, da kuma makamai."

Babu daƙile 'yancin faɗar albarkacin baki, babu ƙarfa-ƙarfa

Haka nan sabon shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta zamo "mai tuntuɓa da neman shawarwari, ba wadda za ta dinga ƙaƙaba wa mutane abin da ba sa so ba".

Ya ce "Gwamnatinmu za ta yi jagoranci ba mulaka'u ba. Za mu yi tuntuɓa da tattaunawa, ba za mu yi ƙarfa-ƙarfa ba."

Game da 'yancin faɗar albarkacin baki kuwa, ya ce: "Za mu nemi gudummawar kowa, amma ba za mu ware wani ba kawai saboda ra'ayinsa ya saɓa da namu ba."

Zan ci gaba da mutunta ƴan adawa

Shugaba Tinubu ya nuna cewa matakin da masu adawa da nasarar da ya samu a zaɓen suka ɗauka na zuwa kotu haƙƙinsu ne kuma bai ga laifin hakan ba.

"Za su ci gaba da kasancewa 'yan ƙasa kamar ni, kuma zan ci gaba da kallonsu a hakan," a cewarsa.

"Sun zaɓi su kai kukansu kotu. Neman adalci a kotu haƙƙinsu ne kuma ba na ganin laifin yin hakan saboda hikimar kafa dokoki ke nan."

Haka nan, ya ce nasarar da ya samu "ba ta fifita shi sama da sauran ba, sannan kuma hakan bai rage musu matsayi ba a matsayin 'yan Najeriya".

Saƙo na musamman ga masu zuba jari

Ɗaya daga cikin fannonin da ake sa ran Tinubu zai fi mayar da hankali a gwamnatinsa shi ne batun zuba jari da tattalin arziki baki ɗaya, saboda fannin da ya fi ƙwarewa ke nan.

A jawabin nasa, ya faɗa wa masu zuba jari na gida da ƙasashen waje wani saƙo na musamman "Gwamnatinmu za ta nazarci dukkan ƙorafe-ƙorafenku game da yawan karɓar haraji iri-iri da kuma sauran tsare-tsaren da ke hana zuba jari."

Ya ci gaba da cewa: "Za mu tabbatar masu zuba jari da kamfanonin ƙasashen waje sun samu damar kwashe kuɗinsu na halak da ribarsu zuwa gida."