You are here: HomeAfricaBBC2023 12 08Article 1895279

BBC Hausa of Friday, 8 December 2023

Source: BBC

' Mu na rayuwa cikin zulumi sakamakon hare haren 'yan bindiga'

Hoton alama Hoton alama

Al’ummar garin Kidandan, da ke ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, sun koka kan yadda ‘yan bindiga suka hana su sukuni, sakamakon hare-haren da suke kai musu da kuma karbar haraji kafin zuwa gona.

Sun ce sun shafe tsawon watani 'yan bindgar na kai mu su hare -hare wanda a wasu lokutan sukan hallaka mutane.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce a yanzu ‘yan bindiga kan ci karensu ba bu babbaka ba tare da jami’an tsaro sun taka mu su birki ba kamar yadda wani mazauni yankin ya shaidawa BBC:

“ Wani lokaci idan suka zo, za su yi harbe -harbe daddare kawai su fita, wani lokacin idan sun samu sa’a sukan ajiye baburansu a bayan gari, su shigo cikin gari su dauki mutane,” in ji shi.

Mazaunin yankin ya ce ko a baya baya nan sai da suka dauki wani matashi wanda yake wa kasa hidima wanda ya mallaki shagon kemis. Ya ce alamarin ya sa mutane na rayuwa cikin zulumi.

"Mutane ba sa iya barci duk da cewa akwai jami'an tsaro amma ana ganin 'yan ta'adan da tsakar rana kuma baka da halin da za ka ce za ka kai wa wani farmaki saboda reshe zai iya juyawa da mujiya”

"Sannan ba ka isa kana da gona a cikin gari, ka ce zaka je gyra amfanin gonarka matukar ba ka sami daya daga cikin wakilansu ba na cikin gari ka danga mi shi na goro , sannan ya baka dama ya tura mutanensu aje a ba ka tsaro har ku je a samu abinda ake so na amfanin gona" in ji shi .

Shi ma dai wani mazaunin yanki ya shaida wa BBC suna cikin matsananciyyar damuwa:

"Ko dare ya y i za su shigo su dauki mutum, dole mutane su bar gari a irin wannan yanayi saboda akwai wani kauye da kashi biyu na yawan alummar wurin sun tashi", in ji shi

Mazauna yankin sun ce fatansu shi ne mahukutan za su turo da karin jamian tsaro zuwa Giwa domin a bai wa mutane cikin garin tsaro.

Rundunar ‘yansandan jihar Kaduna ta danganta matsalar tsaro da ake fuskanta a Giwa akan rashin samun bayyanan siri daga mazauna yankin a kan lokaci. ASP Mansir Hasan shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna

"Bama samun bayyanan sirri da wuri , wani zubin har sai lokacin da mutane suka shigo , za a gansu za su yi wasu abubuwa har sai lokacin da su ka yi kokarin daukar mataki ko na hari daga alumma daga wannan lokacin ne za ka ga na bamu wannan bayanan sirri", in ji shi

ASP Hasan ya ce ko a baya bayyan sun zauna da mahukantan yankin da suka hada da shugaban karamar hukumar ta Giwa da 'yan majalisunsu inda sun tattauna a kan irin matakin daya kamata a kara dauka domin tabbatar da tsaro a yankin