You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845878

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

'Mu na cikin mawuyacin hali a Sudan'

Hoton alama Hoton alama

Rahotanni daga Sudan sun ce, har yanzu wasu 'yan Najeriya kusan dari su na can a makale, su na jiran a kwaso su zuwa gida.

Sun ce sun kasa ficewa daga kasar sakamakon yakin da ake yi a Sudan.

'Yan Najeriyan, sun ce su na cikin mawuyacin hali sakamakon matsalolin karancin abinci da ruwan sha da kudi da sauran kayan bukatun rayuwar yau da kullum.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta yi alkawarin za ta kwashe su, ta mayar da su gida, amma yanzu haka an yi watanni biyu su na jira, kuma babu wani labari game da hakan.

Yanzu haka akwai ‘yan Nijeriya 85 wadanda suka kunshi maza 60 da mata 25 da kuma kananan yara da suka makale a garin Bar-Sudan na gabar tekun Bahar Maliya a gefen kasar su na can su na dakon a mayar da su gida Nijeriya sakamakon yakin da ake tafkawa tsakanin bangarorin sojin kasar.

Daya daga cikin ‘’ yan Najeriyar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa tun watanni biyu da suka gabata ne suka makale a garin .

“ An zo an kwashi mutane a jirgin da ya tafi na karshe, aka ce mu da mu ka rage (maza ) mu yi hakuri, a kwashe mata bakidaya, idan sun je za a dawo a daukemu“, in ji shi.

Ya ce shi da sauran mutane su na zaman jiran a zo a kwashesu amma har yanzu ba a turo ba kuma a yanzu sun shafe tsawon watan biyu cif-cif da faruwar alamarin.

Sai dai ya bayyana cewa suna cikin wani mawuyacin hali:

“Mu na bukatar taimako fiye da yadda ake tunani, akwai matsalar yunwa, ba wurin kwana, ruwan da ake amfani da shi ruwa ne mai gishiri, kuraje sun feso wa mutane da dama a jiki, mutane da dama ba su da lafiya ga kuma rashin kudi“.

Akwai kungiyoyin agaji da ke taimaka mu su da abinci amma sau daya su ke kawo wa a rana kuma kwantaragin aikinsu ya zo karshe a cewarsa. Sun kuma yi ikirarin cewa tafiya a kasa na cike da hadari.

”Duk wanda ya san Sudan ya san yaki ake yi a kasar, wurare kalilan ne yakin bai shafa ba, kuma akan hanya kadai za ka hadu da jami'an tsaro daban -daban, kuma sauran hanyoyin da za ka yi amfani da su, ba za ka iya bi ba saboda su ma ana yaki a wadanan wurare.

BBC ta kira jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya mai kula da batun kwaso ‘yan Nijeriya daga Sudan amma bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Haka kuma bai ce uffan ba game da sakon da aka aike masa ta waya.