You are here: HomeAfricaBBC2021 04 03Article 1222963

BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: bbc.com

Mu muka harbi jirgin sojin Najeriya - Boko Haram

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani faifen bidiyon da ke nuna cewa ita ta harbo jirgin sojin saman Najeriya a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Faifen bidiyon ya nuna mayakan dauke da makaman harbo jirgin da masu cin dogon zango, da kuma tarkace da gawar matukin jirgin.

Duk da cewa babu wata majiya da ta bayyana sahihancin wannan bidiyo amma ya nuna yadda jirgin ya kama da wuta daga sama yayin da yake kokarin fadowa,

Ana kuma iya ganin daya daga cikin mayakan a tsaye a gefen tarkacen jirgin da yake ci gaba da cin wuta.

Kawo yanzu dai ba a samu wani martani daga bangaren rundunar sojin Najeriyar ba game da wannan ikirari na kungiyar ta Boko Haram.

A ranar Laraba ne rundunar sojin saman a wata sanarwa da kakainta Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, ta bayyana bacewar jirgin na ta mai kirar Alfa Jet (NAF 475) mai dauke da mutum biyu.

Kuma tun da misalin karfe biyar na yammacin Laraba 31 ga watan Maris ne aka daina jin duriyar jirgin.

Aikin da jirgin ke yi dai wani bangare na taimakawa ci gaba da yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

A watan Fabrairun da ya gabata ma wani jirgin yaƙin rundunar sojin saman ƙasar ya yi hatsari a Abuja a kan hanyarsa ta zuwa Minna, inda dukkan jami'ai bakwai da ke cikinsa suka mutu.

Join our Newsletter