You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824758

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

Source: BBC

Mohamed Bazoum: Daga gadon mulki zuwa ɗaurin talala

Mohamed Bazoum, shugaba da anka cire a mulki Mohamed Bazoum, shugaba da anka cire a mulki

A ranar Lahadi ne sojojin mulkin Nijar suka ba da sanarwar cewa za su gurfanar da Shugaban Nijar Mohamed Bazoum a gaban kotu bisa zargin cin amanar ƙasa.

Sun kuma tuhume shi da yi wa tsaron cikin gida da na wajen ƙasar zagon ƙasa.

Lamarin na zuwa ne yayin da Bazoum ya shiga kwana na 18 tun bayan da sojojin suka tsare shi a ranar 25 ga watan Yuli, kafin su sanar da kifar da gwamnatinsa a ranar 26.

Ga wasu abubuwa da game da yadda hamɓararren shugaban ya hau da kuma sauka daga mulki.

Ministan da ya zama shugaban ƙasa

Bazoum mai shekara 63 ya riƙe muƙamin ministan harkokin waje da na cikin gida ƙarƙashin gwamnatin Mahamadou Issoufou.

Issoufou ya sauka daga mulki bayan yin wa'adi biyu na shekara biyar-biyar, kuma ya zaɓo Bazoum a matsayin ɗan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya.

Nasarar Bazoum a zaɓen 2021 ta kasance zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula ta farko a Nijar da ta karɓi mulki daga irinta.

An yi juyin mulki sau huɗu a baya tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960 daga ƙasar Faransa.

Ƙalubalen tsaro

Bazoum ya gaji matsalar tsaro kuma ya yi alƙawarin ɗorawa kan tsare-tsaren gwamnatin Issoufou na daƙile hare-haren masu iƙirarin jihadi, da kuma rage talauci a ƙasar da ke cikin mafiya talauci a duniya.

Nijar na maƙwabtaka da wuraren da aka fi fama da tashin hankali - ɗaya a kusa da iyakarta da Mali da Burkina Faso ta yammaci, inda 'yan bindigar da ke ƙawance da al-Qaeda da Islamis State ke kai hare-hare, ɗayar kuma a iyakarta da Najeriya ta kudanci, inda Boko Haram ke ayyukanta.

Nijar ta ƙarfafa alaƙarta da ƙasashen Yamma a ƙarƙashin gwamnatin Bazoum, har ma ta zama cibiyar dakarun Faransa da Amurka da Italiya da Jamus.

Shugabannin juyin mulkin sun bayyana matsalar tsaro a matsayin dalilin da ya sa suka kifar da gwamnatin, amma alƙaluma game da matsalar sun nuna cewa hare-hare sun ragu sakamakon matakan gwamnatin Bazoum ɗin da kuma taimakon dakarun ƙasashen waje.

Gwagwarmayar neman iko

Ana alaƙanta juyin mulkin na ranar 26 ga Yuli da rashin jituwa tsakanin Bazoum da wani ɓangare na rundunar sojin ƙasar, a cewar cibiyar International Crisis Group.

'Yan kwanaki kafin rantsar da Bazoum a matsayin shugaban ƙasa a 2021, wata runduna ta yi yunƙurin kifar da gwamnati ta hanyar karɓe iko da fadar shugaban ƙasa.

A lamari na baya-bayan nan, yunƙurin Bazoum na raba wasu manya da muƙamansu a rundunar soja da kuma gwamnatinsa ya taka rawa wajen kifar dagwamnatin tasa da Janar Abdourahamane Tchiani ya yi, wanda shi ne shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa Reuters.

Tsare Bazoum

Tun bayan kifar da gwamnatinsa, sojoji ke tsare da Bazoum cikin halin da jam'iyyarsa ta bayyana da "na rashin imani", ba tare da ruwan sha ba, ko wutar lantarki, ko kyakkyawan abinci.

An tsare shi tare da ɗansa da matarsa.

Ƙasashen Afirka da na duniya sun yi kiran a sake shi.

A ranar Litinin, 13 ga watan Agusta sojojin mulkin suka ce sun tattara hujjojin da za su tuhumi Bazoum ɗin bisa "cin amanar ƙasa da kuma yi wa tsaron ƙasa zagon-ƙasa".

Rahoto daga Reuters