You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806401

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Messi zai buga wasan farko a Inter Miami cikin watan Yuli

Lionel Messi Lionel Messi

Lionel Messi zai fara yi wa Inter Miami tamaula a karawar da za ta buga a League Cup da Cruz Azul ranar 21 ga watan Yuli.

Kyaftin din tawagar Argentina ya saka hannu da kungiyar da ke buga gasar Amurka kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar 2025.

Mai rike da kyautar Ballon d'Or, mai shekara 36 ya bar Paris St Germain, bayan kammala kakar 2022-23.

Messi ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya a bara kuma Ballon d'Or na bakwai, wanda ake hasashen shi ne zai karbi na bana, bayan da ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

Dan wasan ya ci kwallo 32 a karawa 75 da ya yi wa PSG, wanda ya ci kwallo 16 ya bayar da 16 aka zura a raga a kakar Ligue 1 da ta wuce.

Messi ya koma taka leda a Faransa a 2021, bayan da ya yi shekara 21 a Barcelona.

Dan wasan shi ne kan gaba a yawan ci wa Barcelona kwallaye a tarihi mai 672, wanda ya lashe kofin La Liga 10 da Champions League hudu da Spanish Cup bakwai.