You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1760756

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Messi zai bar PSG a karshen kakar wasanni ta bana

Lionel Messi ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a Paris a cikin 2021 Lionel Messi ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a Paris a cikin 2021

Lionel Messi zai bar Paris St-Germain a bazara a lokacin da kwantiraginsa na yanzu zai kare.

Ɗan wasan wanda ya lashe Gasar cin Kofin Duniya da Argentina, ya so ya tsawaita zamansa na shekara guda amma shi da PSG ba sa son saka hannu kan yarjejeniyar.

Messi bai gamsu da cewa kungiyar za a iya fafatawa da ita ba a Gasar Zakarun Turai, inda PSG ke son mayar da hankali wajen bunkasa hazikan matasa.

Ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a birnin Paris a shekarar 2021 tare da zaɓin sabunta kwantiragin na shekara ɗaya.

An fahimci cewa mahaifin Messi, Jorge ya sanar da PSG hakan makwanni da suka gabata.