You are here: HomeAfricaBBC2023 05 04Article 1761035

BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Messi zai bar PSG, Man United ta yi tanadi idan ta rasa Kane

Lionel Messi Lionel Messi

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi zai bar Paris St Germain, bayan da kungiyar Faransa ta yanke shawarar ba za ta tsawaita zamansa ba. (Foot Mercato - in French)

Manchester United ta tanadi ‘yan wasa uku da za ta taya koda ba ta samu daukar dan kwallon Tottenham, Harry Kane, sun hada da mai tka leda a Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani da na Roma, Tammy Abraham da dan kwallon Inter Milan, Lautaro Martinez, 25. (FourFourTwo)

Tattaunawar da Tottenham ke yi kan daukar tsohon kociyan Bayern Munich, Julian Nagelsmann ta ci karo da cikas, bayan da kungiyar ba ta da tabbas kan daukar daraktan kungiyar. (Telegraph - subscription required)

Sam Allardyce na tattaunawa da Leeds United kan zama kociyan kungiyar an kuma yi masa tayin ladan fam miliyan daya idan kungiyar za ta ci gaba da zama a Premier a badi a karkashinsa. (Star)

Allardyce zai samu bonus sama da fam miliyan 2.5 idan Leeds ba ta fadi daga Premier League ba, tuni ya kira tsohon kociyan Oxford United Karl Robinson domin ya taimaka masa. (Times - subscription required)

Masu Chelsea Todd Boehly da Behdad Eghbali sun gana a Los Angeles a makon jiya kan batun daukar tsohon kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino domin bashi aikin jan ragamar kungiyar Stamford Bridge (Evening Standard)

Shugaban Arsenal, Stan Kroenke zai bai wa kociyan Gunners Mikel Arteta £200m domin ya kara karfin kungiyar wajen sayo sabbin ‘yan kwallo a kakar mai zuwa. (Football Transfers)

West Ham ta fara tsara yadda za ta dauki dan wasa mai buga tsakiya, bayan da Declan Rice zai hakura da kungiyar. (Football Insider)

Ajax ta yiwa mai tsaron baya Jurrien Timber farashin fam miliyan 44, wanda ake alakanta shi da komawa ko Liverpool ko kuma Manchester United. (Sky Sports Germany)

Tottenham da Arsenal za suyi rige-rigen sayen dan Crystal Palace, Marc Guehi. (Evening Standard)

A shirye Bayern Munich take ta sayar da Sadio Mane ga duk kungiyar da ke bukatar dan kwallon a karshen kakar nan. (90 Min)

Kociyan Juventus, Massimiliano Allegri y ace fatan da suke su buga Champions League a badi tsarin da suke kai kenan – sai dai Angel di Maria da Rabiot, yarjejeniyarsu za ta kare a karshen kakar nan. (Football Italia)

Fulham na fatan kulla yarjejeniya da Leeds United kan mallakar Dan James, 25. (Football Insider)