You are here: HomeAfricaBBC2023 08 07Article 1820219

BBC Hausa of Monday, 7 August 2023

Source: BBC

Messi ya sake cin kwallo biyu a Inter Miami

Lionel Messi Lionel Messi

Lionel Messi ya zira kwallo biyu a raga inda ya taimaka wa Inter Miami samun gagarumar nasara a kan FC Dallas har ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar kofin Leagues ranar Lahadi.

Dallas na kan gaba a wasan da ci 4-2, kafin Miami ta ci kwallo biyu cikin minti goman karshe na wasan inda aka kai ga bugun fenariti.

Miami ta yi nasara a bugun fenariti da ci 5-3 a filin wasa na Toyota da ke Frisco, Texas.

Tsohon dan wasan gaban Barcelona da Paris St-Germain ne ya fara zira kwallo a raga bayan mintuna shida, kafin a ci kwallo na biyu a minti 85.

Kafin zuwan Messi Miami, ƙungiyar ba ta yi nasara ba a wasanni 11 da ta buga amma yanzu sun yi nasara sau hudu a jere.

Inter Miami ce kungiya ta farko da ta samu gurbi a matakin daf da na kusa da na karshe a gasar kofin Leagues, wanda aka fara a shekarar 2019 kuma ya hada da kungiyoyi daga Amurka da Mexico.