You are here: HomeAfricaBBC2023 08 21Article 1829141

BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Messi ya daukar wa Inter Miami kofin farko a tarihi

Lionel Messi Lionel Messi

An yaba wa Lionel Messi a matakin ''fitatcen dan kwallon duniya, bayan da ya ci kwallo na 10 a wasa bakwai da ta kai Inter Miami ta dauki kofi a karon farko.

Mai shekara 36 ya fara cin kwallo a karawar daga wajen da'ira ta 18 da ya bai wa Inter jan ragamar Nashville SC a wasan karshe a Leagues Cup final.

Daga baya Fafa Picault ya farke da ta kai wasan zuwa bugun fenariti, duk da karin lokaci da suka tashi 1-1.

Miami ta lashe kofin da cin 10-9, bayan da Drake Callender ya tare kwallon golan, Nashville, Elliot Panicco.

Miami tana da mummuna tarihi a Major League Soccer a bana, amma ta dauki kyaftin din Argentina Messi da Jordi Alba da kuma Sergio Busquets daga Barca.

Yanzu ta yi wasa bakwai a waje ba tare da an doke ta ba, sannan ta lashe kofin da ake buga shi tsakanin kungiyoyin gasar Amurka da ta Mexico.

Wannan shi ne karon farko da Miami ta dauki kofi tun bayan da aka kafa kungiyar a 2020.

Suna da wata damar kai wa karawar karshe, idan suka fafata da Cincina a wasan daf da karshe ranar Laraba a US Open Cup.

Messi, wanda shine aka zaba dan kwallon da ya fi taka rawar gani a gasar ya dauki kofi na 44 - shi ne kan gaba a aukar kofi, fiye da duk wani dan kwallon duniya.