You are here: HomeAfricaBBC2023 07 26Article 1812797

BBC Hausa of Wednesday, 26 July 2023

Source: BBC

Messi ya ci ƙwallo biyu a wasan da Inter Miami ta doke Atlanta

Lionel Messi Lionel Messi

Lionel Messi ya ci kwallo biyu kuma ya bayar da daya aka zura a raga a karawar da Inter Miami ta doke Atlanta United da ci 4-0.

Kyaftin din tawagar Argentina, mai shekara 36 ya fara zura ƙwallo ne a minti na 22 da fara tamaula, daga baya ya bai wa Robert Taylor kwallo ya zura a raga.

Bayan da Messi ya ci kwallo na biyu ne sai ya nuna mamallakin Inter Miami, David Beckham, wanda ya kalli fafatawar.

Kwazon da Messi ya nuna ya biyo bayan wasan farko a makon jiya da ya fara buga wa kungiyar, da cin kwallo a bugun tazara.

Messi mai Ballon d'Or bakwai ya yi atisaye da 'yan wasan Inter Miami a makon jiya, bayan da ya koma kungiyar da ke buga Major League Soccer daga PSG.

Wanda ya lashe kofin duniya a 2022, ya ci kwallo 32 a wasa 75 a kaka biyun da ya yi wa kungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Faransa ta Ligue 1.

An sauya Messi daga karawar a minti na 78, inda magoya baya suka yi ta masa tafi a filin da ke cin 'yan kallo 20,00 wato DRV PNK Stadium.