You are here: HomeAfricaBBC2023 06 05Article 1780610

BBC Hausa of Monday, 5 June 2023

Source: BBC

Messi da Ramos sun buga wasan karshe a PSG

Yan wasan PSG Yan wasan PSG

Lionel Messi da Sergio Ramos sun buga wa Paris St-Germain wasan karshe ranar Asabar a karawar Ligue 1 da Clermont.

Mai tsaron baya, Ramos ya fara cin kwallo daga tamaula da Vitinha ya buga masa, sannan Kylian Mbappe ya kara na biyu a bugun fenariti.

Clermont ta zare daya ta hannun Johan Gastien, sannan Mehdi Zeffane ya farke ta biyu. Sai kuma Grejohn Kyei, wanda tun farko ya ci kwallo aka farke, ya kuma barar da fenariti, shi ne ya ci na uku.

Messi, kyaftin din Argentina, wanda magoya baya suka yi wa ihu a lokacin da ake gabatar da 'yan wasa, ya barar da damar makin cin kwallaye.

Tsohon dan kwallon Barcelona ya ci wa PSG kwallo 32 a wasa 75.

Ramos, tsohon mai tsaron bayan Real Madrid, kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana, inda PSG ta ce ba za ta tsawaita zamansa ba, bayan da yake fama da jinya.

Watakila Messi zai koma taka leda a Al Hillal ta Saudiyya ko kuma Inter Miami mai buga gasar kwallon Amurka ta Major League Soccer.

'Yan wasan PSG kowanne ya saka riga mai dauke da sunan Ramos, amma kowanne da lambar da yake sawa.

Kwallon da Mbappe ya ci Clermont ranar Asabar ya sa ya zama kan gaba a cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Faransa ta Ligue 1 karo biyar a jere.

Mbappe ya zama na hudu da ya lashe kyautar takalmin zinare karo biyar a jere, bayan Carlos Bianchi da Delio Onnis da kuma Jean-Pierre Papin.

Dan wasan tawagar Faransa ya zira 29 a raga a bana, ya dara dan wasan Lyon Alexandre Lacazette da tazarar biyu a raga.