You are here: HomeAfricaBBC2023 01 18Article 1697681

BBC Hausa of Wednesday, 18 January 2023

Source: BBC

Mene ne manufar Birtaniya na tura masu neman mafaka zuwa Rwanda?

Tutar Rwanda Tutar Rwanda

Gwamnatin Birtaniya na shirin tura wasu daga cikin masu neman mafaka zuwa Rwanda. Babbar kotun ƙasar ta ce shirin halastacce ne, sai dai matakin na fuskantar ƙalubalanta a kotunan ƙasar.

Me tura masu neman mafaka zuwa Rwanda ke nufi?

Matakin zai bayar da dama domin tura wasu masu neman mafaka a Birtaniya zuwa Rwanda domin samun mafakar a can.

Za su iya zama a Rwanda a matsayin 'yan gudun hijira. ko kuma su nemi izinin zama a ƙasar bisa wasu sharuɗa, ko kuma su nemi mafakar da kashin kansu.

Gwamnatin Birtaniya ta ce matakin zai rage kwararar masu neman mafaka zuwa Birtaniya ''ba bisa ƙa'ida ba, ta ɓarauniyar hanya, kamar shiga ƙasar ta hanyar amfani da ƙananan jiragen ruwa."

To sai dai tun bayan bayyana matakin ranar 14 ga watan Afrilu adadin mutanen da ke shiga Birtaniya domin neman mafaka bai ragu ba.

A shekarar 2022 yawan mutanen da suka je Birtaniya ya haura 45,000 adadi mafi yawa tun bayan da aka fara ƙididdige yawan masu shiga ƙasar don neman mafaka.

Shin matakin yana kan doka?

Masu adawa sun ce Rwanda ba ta da tsaron da ya kamata a kai masu neman mafaka, dan haka shirin ya saɓa dokokin 'yancin ɗan adam.

To amma a watan Disamba babbar kotun ƙasar ta ce shirin yana bisa doka. Tana mai cewa shirin kai masu neman mafaka zuwa Rwanda bai saɓa wa dokokin 'yan gudun hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya ba.

Haka kuma a ranar 16 ga watan Janairun da muke ciki, babbar kotun ta yanke hukuncin cewa ƙungiyoyin da ke adawa da matakin kuma suka samu rashin nasara a kotun na da damar ɗaukaka ƙara game da wani ɓangare na hukuncin.

Hakan na nufin babu jirgin da zai fara jigilar masu neman mafakar yayin da batun ke gaban kotun ɗaukaka ƙara. Dan haka babu ranar fara jigilar.

Mutum nawa za a tura neman mafaka zuwa Rwanda?

A baya gwamnatin Birtaniya ta ce ''duk mutumin da ya shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba'' bayan ɗaya ga watan Janairun 2022 za a tura su, ba tare da ƙayyade adadi ba.

Ƙasar Rwanda ta ce za ta karɓi masu neman mafaka 1,000, kuma tana da damar karɓar fiye da haka.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, Rwanda za ta buƙaci Birtaniya ta miƙa mata wasu daga cikin 'yan gudun hijirarta. Haka kuma ta ce babu mai neman mafaka ko ɗaya da aka tura ƙasar kawo yanzu.

An tsara cewa jirgin farko zai tashi da masu neman mafakar zuwa Rwanda cikin watan yuni, to amma an soke shirin bayan da aka ƙalubalanci matakin a gaban kotu.

Kamfanin jirgin sama na 'Privilege Style' - wanda aka tsara a baya cewa shi zai yi jigilar masu neman mafakar - ya bayyana ficewa daga yarjejeniyar bayan da ƙungiyoyin kare hakkin 'yan gudun jihira suka fara kiraye-kiraye.

Kuɗin da shirin zai laƙume?

Kawo yanzu Birtaniya ta biya gwamnatin Rwanda fam miliyan 140 game da shirin.

Sauran abubuwan da za su laƙume kuɗi sun haɗa da zirga-zirgar fasinjojin a jiragen sama, da abinci, da matsuguni, da kudin da za a riƙa biyan masu yi musu tafinta.

Tsarin neman mafaka na Birtaniya na laƙume kimanin fam biliyan 1.5 a duk shekara. Haka kuma ana kashe kusan fam miliyan bakwai na otal da matsuguni ga masu neman mafaka a kowace rana

Masu suka na cewa kuɗaɗen da shirin zai laƙume sun yi yawa saboda lokacin da aka ɗauka kafin ɗaukar mataki kan buƙatar hakan.

Shin wane ne mai neman mafaka?

Hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana mai neman mafaka da cewa shi ne wanda ke neman matsuguni da kariya a wata ƙasar.

Ta kuma bayyana ɗan gudun hijira da cewa shi ne mutumin da ya gujewa yaƙi ko tashin hankali da muzgunawa a ƙasarsa.

Dokokin duniya sun kare 'yancin 'yan gudun hijira. To sai dai ya rage wa ƙasar da masu neman mafakar suka je da ta ba su matsayin 'yan gudun hijira.

Daga farkon shekarar da ta gabata zuwa watan Sataumba Birtaniya ta karɓi takardun buƙatar masu neman mafaka 72,027.

Wannan kuma shi ne adadi mafi yawa cikin kusan shekara 20.