You are here: HomeAfricaBBC2023 03 30Article 1740767

BBC Hausa of Thursday, 30 March 2023

Source: BBC

Mece ce gwamnatin riƙon-ƙwarya da 'wasu ke son kafawa' a Najeriya?

'Yan sandan cikin gida sun tabbatar da cewa akwai wani shiri na kafa gwamnatin rikon kwarya 'Yan sandan cikin gida sun tabbatar da cewa akwai wani shiri na kafa gwamnatin rikon kwarya

A ranar Laraba ne hukumar ƴan sandan ciki ta Najeriya ta tabbatar da raɗe-raɗin da ake yi cewar akwai wata ƙullaliya ta ganin an kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya a ƙasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunaya ya sanya wa hannu ta ce “wani yunƙuri ne na jingine kundin tsarin mulki da yin zagon ƙasa ga mulkin farar hula da kuma yunƙurin jefa ƙasar cikin ruɗani.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “masu kitsa lamarin sun tattauna kan hanyoyi da dama na aiwatar da shirin nasu, kamar haddasa mummunar zanga-zanga a manyan biranen Najeriya, wadda za ta haifar da ƙaƙaba dokar-ta-ɓaci.”

“Ko kuma ta hanyar nemo izinin kotu domin dakatar da rantsar da sabuwar gwamnati da majalisar dokokin tarayya, ta hanyar da ba ta dace ba.”

Ma'anar gwamnatin riƙon-ƙwarya?

Gwanatin riƙon-ƙwarya na nufin gwamnatin wucin-gadi ko kuma gwamnatin da ake kafawa na wani ɗan lokaci.

Wasu kuma kan kiran ta gwamnatin miƙa mulki.

Ana kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ne domin ta yi aiki kafin samar da gwamnati mai zuwa.

A mafi yawan lokuta babban aikinta shi ne tsara harkokin siyasa da kuma yadda za a yi zaɓe domin samar da sabuwar gwamnati mai zuwa.

Manyan masu riƙe da lamurran ƙasa ne ke zaɓen waɗanda za su jagoranci irin wannan gwamnati, mafi yawan lokuta a sa’ilin da aka kawo ƙarshen yaƙin basasa.

Haka nan akan kafa irin wannan gwamnati a lokacin da aka soke zaɓe a ƙasar da ke bin tafarkin demokuraɗiyya, bayan cikar wa’adin gwamnati mai ci.

A Najeriya an kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙarshe ne shekaru 30 da suka gabata, a 1993, lokacin da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaɓen da aka gudanar, wanda ake yi wa laƙabi da June 12.