You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776788

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Me za a tsammata a sabon wa'adin mulkin Shugaba Erdogan?

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Recep Tayyip Erdogan bai yi nasara wurin rerawa magoya bayansa wakar murnar lashe zabe mai zaki ba - amma muryarsa na da zaki ta fannin sanin kimiyyar fafatawa a fagen siyasa.

Ya karanci masu jefa ƙuri'a fiye da masu zabe da manazarta, wadanda suka ce ‘yan adawa za su iya doke shi. To, ba dai a wannan karon ba.

Abokin hamayyarsa - Kemal Kilicdaroglu - yana bayansa da kashi 4 cikin 100 ne kacal a sakamakon zaben da ya gudana. Babu shakka shugaba Erdogan zai zurfafa tunani a kan haka yayin da zai fara wa'adinsa na uku a kan karagar mulki.

Wannan kasar mai muhimmanci ga kungiyar NATO ta zabi gogaggen dan mulkin kama-karya maimakon dan dimokradiyya, wanda ba a taba gwada shi ba kamar Mista Kilicdaroglu.

Shugaban 'yan adawan ya gudanar da yakin neman zabensa a matsayin mutumin kirki wnda daga farko ya yi wa 'yan Turkiyya alkawarin sabon yanayi. Daga baya ya karkata, yana mai shan alwashin mayar da dukkan ‘yan gudun hijira gida. Hakan ya sama masa ƙarin goyon bayan masu kishin ƙasa, amma hakan bai sa ya kai labari ba.

Shugaba mai akidar Musulunci, Erdogan na da wata alaka ta musamman da mabiyansa wanda aka yi shekara 20 ana gina ta. Mafi yawansu masu ra'ayin addini ne irin nasa. Kuma sun kasance tare da shi a kowanne hali - duk da hauhawar farashin kaya - sun sake kara masa shekara biyar.

A yayin da aka sanar da sakamakon zabe zagaye na biyu, titunan birnin Ankara sun cika da tutocin Turkiyya, da karar hon din motoci, tare da dandazon magoya bayan Erdogan.

Mutane da dama sun yi tururuwa zuwa fadarsa ta musamman mai sama da dakuna 1,000, wadda kuma abokin hamayyarsa ya yi alkwarin zai mayar da ita ta amfanin jama'a.

"An albarkace mu, shugabanmu zai sake jagorantar mu," in ji Hatice Duran wata mai shekara 50 da haihuwa, wacce ke murmushi sanye da lullubi.

"Babu wani abin da ya fi wannan daɗi, duniya ta ji haka. Shi ne shugaban da ya bijire wa duniya baki daya, ya koya wa duniya darasi."

Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka sa shi farin jini: Mista Erdogan shugaba ne mai zafin nama, wani shugaban Musulunci na zamani wanda ba ya saurara wa kowa.

Abin da zaben nan ya nuna shi ne mafi yawan mutane sun fi son mutum mai tsauri kan mutumin kirki.

Yanzu ya kara samun kwarin gwiwa. 'Yan adawar kasar sun sha mummunan kaye kuma Fadar Kremlin ta Rasha ta yi murna da hakan.

Wannan shi ne sakamakon da Shugaba Vladimir Putin ya so - ba abin mamaki ba ne da ya kasance daya daga cikin wadanda suka fara taya shugaban na Turkiyya murna.

Mista Putin ya yi iyakacin kokarinsa don ganin abubuwa sun yi masa sauki, gami da jinkirta biyan dala miliyan 600 na iskar gas na Rasha.

Mista Erdogan ya shiga gasar tare da ƙudirori da yawa: yana da dabara, ya san yadda zai bi da talakawa kuma yana da iko a kan kashi 90 cikin 100 na kafafen yada labarai da ke ƙasar.

A jawabinsa na nasara, ya dage kan cewa 'Tukiyya ce kadai ta yi nasara'- amma bai bata lokaci ba wurin sukar 'yan adawa da kungiyar masu neman jinsi daya (LGBTQ+).

Kungiyoyin biyu na iya fuskantar hare-hare kuma ana iya samun karin takura kan 'yancin dan Adam da kuma 'yancin fadar albarkacin baki cikin shekaru masu zuwa.

Akwai karancin masu sa ido a can, kuma ba a san dadadden shugaban kasar na Turkiyya da daga kafa ba.

wadanda suka bukaci canji - kusan kashi 48 cikin 100 na masu zabe- za su yi takaici, kuma kila su kasance cikin tsoro.

Mutane da yawa sun yi hasashen cewa za a samu karin addini da kuma karancin 'yanci a rayuwar al'ummar ƙasar, wadda za ta cika shekara 100 da kafuwa a watan Oktoba.

Turkiyya yanzu ta kasance kasar da kawuna suka rarrabu. Masu suka dai na cewa shugaban kasar ba shi da maganin wadannan matsalolin.

A wane yanayi sakamakon zaben ya bar makwabtan Turkiyya da kawayenta na NATO? Za su kasance a ankare, ganin cewa Shugaba Ergdogan na jin dadin rikita yadda abubuwa ke kasancewa a duniya.