You are here: HomeAfricaBBC2023 07 01Article 1795928

BBC Hausa of Saturday, 1 July 2023

Source: BBC

Me ya sa matasan Koriya ba sa son shiga cikin jama'a?

Yoo Seung-gyu Yoo Seung-gyu

A 2019, Yoo Seung-gyu ya fita daga ɗakinsa a karon farko cikin shekara biyar.

Da farko, mutumin mai shekara 30 ya share "hargitsattsen ɗakin" nasa tare da ɗan uwansa. Sannan ya tafi kamun kifi tare da wasu gwagware da ya haɗu da su a wata ƙungiyar ba da tallafi.

"Abu ne baƙo da na gan ni a wajen kamun kifi amma kuma da daɗi bayan shafe tsawon lokaci a keɓe. Kamar ba da gaske ba, amma lallai ni ne am wurin. Ni ne a raye," a cewar Mista Yoo.

Matasa da yawa a Koriya ta Kudu na keɓe kansu daga bainar jama'a.

Waɗannan gwagwaren matasan ana kiran su hikikomori, kalmar da ta samo asali daga Japan a 1990 sakaamakon keɓe kan su da matasa suka dinga yi a loakcin.

Lamarin ya zama babban abu a Koriya ta Kudu, ƙasar da ke fama da ƙarancin haihuwa. Hakan ta sa hukumomi ke bai wa wasu matasa kuɗi da suka kai wani matakin albashi don su fito su yi hulɗa da sauran jama'a.

Matasa 'yan shekaru tsakanin tara zuwa 24 da suka fito daga gida mai matsakaicin samu, za a dinga ba su kuɗin won 650,000 (kwatankwacin dala 490; naira 225,000) duk wata.

Za su iya neman ƙarin tallafi a kan wasu abubuwan daban, ciki har da kiwon lafiya, da ilimi, da neman shawarwari, da ɓangaren shari'a, da sauransu.

An ƙirƙiri waɗannan tallafin ne don "bai wa matasa damar cigaba da rayuwa a cikin jama'a," in ji Ministan Harkokin Iyali da Daidaito.

Amma zuba kuɗi a kan matsalar ba zai magance ta ba, kamar yadda matasan ke cewa bayan sun keɓe kan su.

Mista Yoo yanzu na kula da wani kamfani da ke tallafa wa keɓantattun matasan mai suna Not Scary.

Sai dai ya sha gwagwarmaya kafin ya kai inda yake a yanzu. Ya killace kan sa yana ɗan shekara 19, ya fito tsawon shekara biyu don yin hidimar ƙasa na dole, sannan ya sake komawa tsawon shekara biyu bayan haka.

Park Tae-hong, wani magujin mutanen, ya ce gudun jama'a wani zubin "na taimaka wa wasu mutanen".

"Idan mutum ya yi yunƙurin yin wani asabon abu akwai daɗi, amma kuma dole ne mutum ya shirya gajiya da zaƙuwa. Amma idan kana cikin ɗakinka ba ruwanka da wannan. Amma kuma bai kamata abin ya yi tsayi ba," a cewar ɗan shekara 34 ɗin.

Matasa kusan 340,000 ne 'yan shekarun 19 zuwa 39 na ƙasar - ko kuma kashi 3 na wannan ajin - ana yi musu kallon keɓantattu masu gudun jama'a, in ji cibiyar Korea Institute for Health and Social Affairs mai kula da harkokin zamantakewa.

Bincike ya nuna kuma gidajen da suke da mutum ɗaya a ciki a Koriya ta Kudu su ne kashi ɗaya cikin uku na iyalai a ƙasar a 2022. Kazalika a daidai lokacin, mutanen da suka mutu "su kaɗai" sun ƙaru.

Sai kuma ba kuɗi ne ko rashinsu ba ke sa matasan ƙaurace wa al'umma.

"Masu rayuwa iri-iri ne ke shiga halwar," a cewar Mista Park. "Ina mamakin dalilin da ya sa gwamnati ke alaƙanta abin da kuɗi. Ba kowane mai gudun jama'a ne ke da matsalar kuɗi ba."

"Mutanen da ke cikin talauci ai su ne ya zama dole su yi hulɗa da jama'a."

Wani abu ya fi damun irin waɗannan matasanb shi ne cewa ba su cimma wani abu a rayuwarsu na nasara ba kamar yadda sauran danginsu suke ko kuma abin da suke so ba.

Mista Yoo ya ce ya shiga jami'a ne saboda mahaifinsa ya umarce shi, amma ya daina zuwa bayan wata ɗaya.

"Zuwa makaranta abin kunya ne a wajena. Me ya sa ba za a ba ni 'yancin [zaɓar abin da nake so na karanta ba]? Na ji ba ni wani abin yi," in ji shi.

"Al'adar kunya a Koriya ta Kudu, ita ce ke hana masu gudun jama'a bayyana matsalolinsu," in ji Yoo. "Wata rana kawai na taɓa jin cewa rayuwata gaba ɗayanta kuskure ce, sai na tsame kai na daga mutane kawai."

Lokacin da ya keɓe kansa, ko wurin wanke hannu ba ya zuwa saboda ba ya so ya ga ko ɗaya daga cikin 'yan uwansa.

"Mahaifiyata da mahaifina na yawan yin faɗa tun ina yaro. Hakan ya shafi rayuwata a makaranta - wani lokacin makarantu ba su da daɗi a Koriya, kuma ni ma ban ji da daɗi ba. Ban iya kare kaina ba," kamar yadda Mista Park ya bayyana.

Alawus ɗin da zai iya zama "matakin farko" na maganin matsalar, amma matasan da ke aiki na cewa za a iya amfani da kuɗin wajen wasu ayyukan.

"Mataki na gaba, shi ne a tsara shirye-shirye na kyauta a faɗin ƙasa ga matasa masu guje wa al'umma. Yanzu babu shirye-shiryen masu yawa da matasan za su iya shiga," a cewar Kim Hye Won, babbar darakta a cibiyar PIE for Youth.

Mista Yoo ya ce ya fito daga halwar da ya shiga a hankali kuma bayan ya haɗu da sauran matasa ta hanyar wata ƙungiyar daidaita tunani da yanzu ba ta aiki.

"Bayan na samu tallafi, sai na fara tunanin ba matsalata ba ce kawai, ta dukan al'umma ce," in ji shi.

"Daga baya dai na samu na fito daga halwa a hankali."