You are here: HomeAfricaBBC2023 09 30Article 1853969

BBC Hausa of Saturday, 30 September 2023

Source: BBC

Me ya sa maganin tazarar haihuwa ke haifar da illoli ga mata?

Hoton alama Hoton alama

Magungunan hana ɗaukar ciki sun zama muhimmin al'amari ga ma’aurata, musamman ma mata da ke amfani da su wajen ba da tazarar haihuwa da tsara rayuwar iyali.

Irin waɗannan magunguna, sun ƙunshi hanyoyi daban-daban, kama daga magungunan sha zuwa allurai da robar da ake sanya wa mata a dantsensu, da dai sauransu.

Da yawan mata na ganin fa'idar amfani da magungunan hana ɗaukar ciki, amma wasu sun ce sukan fuskanci matsaloli da dama da ke zuwa bayan amfani da su.

Waɗansu matsalolin da mata ke fuskanta sakamakon amfani da magungunan hana ɗaukar ciki kamar yadda Maryam da Faiza, wasu iyaye mata masu amfani da irin waɗannan magunguna suka shaida wa BBC, su ne; matsalolin al'ada da ƙarin ƙiba da haraswa.

Akwai ma ciwon mama da ciwon kai da da rage sha'awar jima'i da fitowar wani ruwa daga al'aura da dai sauransu.

Waɗannan matsaloli suna kuma haifar da rashin jituwa a tsakanin ma’aurata in ji su.

Ƙalubalen magungunan tazarar haihuwa

Hajiya Maryam, ƴar shekara 34 wadda take da yara 3, ta ce ta kwashe kimanin shekara 8 tana amfani da magungunan ba da tazara a cikin tsarin iyali, wanda ita da mijinta suka amince da shi.

“Na yi aure tun ina da shekara 25, kafin na yi aure, ba ni da wata ƙiba, amma ina shiga ɗakin miji da wata huɗu na ɗauki ciki” in ji Maryam.

“Bayan na haihu da wata takwas, kwatsam sai na sake daukar ciki, wanda ya zo min babu shiri, kuma na san shi ma mijin nawa bai ji daɗin haka ba, amma daga baya sai na yi ɓari.”

“Bayan hakan, sai mijina ya ce ya kamata mu je asibiti mu ga likita saboda a ɗora mu a kan shirin ba da tazarar haihuwa.”

Cikin tsare-tsaren ba da tazara iri daban-daban da likita ya nuna wa ma'auratan, Maryam ta yanke shawarar karɓar allura duk bayan wata uku.

Sai dai allurar farko da aka yi wa Maryam, ta sanya ta amai sosai da ciwon ciki, ko da yake, bayan sati ɗaya ta ji yanayin jikinta ya koma daidai.

“Bayan wata uku, sai na koma asibitin don a yi min wata allura, sai dai ta sake sa ni amai da ciwon ciki.”

Wani ƙalubale da Maryam ta fuskanta shi ne shekara ɗaya da fara yi mata allura, sai ta daina ganin al’adarta a kan lokaci.

"Na zo ma ina ganin al’ada kamar sau ɗaya, a wata uku.”

Da na yi likita ƙorafi, sai ya ce wannan ba matsala ba ce. Da ma abin yana zuwa a hakan.

“Bayan kamar shekara biyu da rabi da fara allurar hana ɗaukar ciki, sai na lura ina ƙiba sosai, ko ina a jikina yana ƙara girma, abin ya fara damu na.”

“Na yi wa miji na ƙorafi cewa alluran hana haihuwan nan, yana sa ni yin ƙiba, amma sai ya ce a’a, ciye-ciyena ne kawai.”

Maryam ta ce har kunyar tafiya take a gidanta idan mijin yana nan saboda ƙibar da take ƙara yi, hakan, in ji ta ya kawo rashin jituwa tsakanin su. Har ta riƙa jin kamar mijinta yana guje mata, kuma ba ya son kusantar ta, saboda mai yiwuwa ƙibar da ta yi.

“Mijina ba ya ce min komai, amma ya taɓa faɗa min cewa na rage ƙarfin sha’awa kuma ni’imata ta ragu.”

“Abubuwa duk sun canza, ba kamar da ba lokacin da yake liƙe min”

Ta ce bayan shekara huɗu tana allura, daga bisani ta sake samun juna biyu, inda at haifi ƴan biyu.

Maryam ta bayyana rashin jin daɗin ta kan ƙibar da alluran hana haihuwan ya sa ta har ya kai ga tana jin kunyar fita kuma ko tana tare da mijin ta, ba ta sakewa yadda ta ke yi da.

Ita kuma Faiza, ƴar shekara 28 ce kuma ƴa’ƴan ta biyu, ta shaida wa BBC cewa ta fara nata da shan magungunan hana haihuwa ne, amma daga fara sha, sai ta zo ba ta ganin al’ada yadda ya kamata.

Ta ce har ya kai ga sau daya a wata shida ta ke ganin al’ada, kuma maman ta ciwo.

“Da na ga matsalolin da nake fuskanta suna yawa, sai na koma asibiti na ce wa likita a canza min tsari,”

“Na ce ina son a gwada min robar da ake sa wa a dantsen, sai aka canza min.”

“Shi da farko babu abin da na ji, ba ammai, ba komai, kuma ban yi wani ƙiba ba, amma bayan wasu watanni, sai na zo ba ni yawan jin sha’awa”

“Na lura da yanayi na yana yawan canzawa, rai na yana saurin ɓaci, ba na son kusantar miji na, ko ya zo nema na, sai da kawai na kwanta masa ya biya buƙatunsa, wanda shima haka ba ya masa daɗi”

“Kuma dole na mu yi amfani da tazarar haihuwa, kuma da yake miji na yana da fahimta sosai, amma duk da haka, yana samun matsala da ni”

“Wata sa’in abin zai yi ƙasa sosai, sai kuma ya sake tasowa”

Fa’iza ta ce lamarin ba ya mata daɗi sosai, kuma ta gode wa Allah da mijin ta ya kasance mai fahimta ne.

Mata da dama na fuskantar matsalolin sauye-sauye daban-daban game da shan magungunan hana haihuwa kuma a lokaci daya, akwai waɗanda ba sa fuskantar wata matsala ko kuma matsalar ba ta tsanani.

Me likita ke cewa?

Dr Kabir Dara, Babban liktan mata a asibtin Dara specialist, Katsina ya shaida wa BBC cewa tabbas magunguna hana haihuwa suna da matsaloli amma wasu abubuwan da ake faɗi basu da alaƙa da waɗannan magungunan.

Ya ce magungunan hana haihuwa wasu sinadare ne saboda haka dole ne wasu mata su sami canje-canje kuma ya danganta da irin macen da za ta dauki irin waɗannan magungunan.

Ya ƙara da cewa shiyasa ake bai wa mutane shawara da su fara tuntuban ƙwararru domin a duba a ga wanne ne ya cancanta su yi amfani da shi.

"Ana raba waɗannan magungunan gida gibu, akwai wanda ita mace ta yi, na wucin gadi ne, za ta iya canzawa kuma ta na iya haihuwa, sai kuma dayan, shine na dindindi, wanda idan mace tayi, ba za ta sake haihuwa ba, kamar daure hannun mahaifa."

"Magungunan hana haihuwa na wucin gadi su ne kamar ƙwayoyi na sha, da allurai, akwai wanda ake sa wa a cikin mahaifa, sai kuma wanda ake sa wa a ƙarƙashin fata, kuma duka sun dangata ne ta ɓangaren iya kwanaki, ko watanni, ko shekaru.

"Kwayoyin maganin hana haihuwa kala kala ne, akwai wanda ake bai wa mace ko da tana shayarwa, wanda shine ya fi dacewa da mata dayawa domin shi yana da sinadare wanda yake kama da na jikin mace"

"Su waɗannan ƙwayoyin suna hana ƙwai ya zo, toh kuma idan ƙwai bai zo ba, babu yadda mace za ta dau ciki, sun fi zama mafi aminci kuma ana shan su kullum."

Amma likitan ya ce matsalolin waɗannan ƙwayoyin shi ne suna iya canza yanayin mace kamar su ciwon kai, kasala, da kuma jin mutum kamar ya ƙumbura, ko ƙiba ko teɓa

Likitan ya ƙara bayani game da canjin yanayin al'ada inda ya ce shi ya fi zuwa ne wajen wanda ake yi na allura ko kuma wanda ake sa wa a ƙarƙashin fata.

Ya ce yanda waɗannan hanyoyi na allura ko sakawa a ƙarƙashin fata suke hana mace ta dau ciki shine hana ƙwai ya zo, amma kuma yana daukan lokaci, kuma hanyar da yake bi shine sanya jikin mahaifa din ya ƙone saboda haka idan jikin mahaifa ya ƙone mace za ta yi wata da watanni ba tayi al'ada ba.

"Idan mace tayi wata da watanni ba ta yi al'ada ba, za ta lura cewa idan ya tashi dawowa, zai iya zuwa gutsu-gutsu."

"Shi wanna ba irin na al'ada bane wanda ake sha kullum, wanna an sanya shi ne kawai, yana daukan lokaci kafin ya fara aiki, yanayin jinin jikin mutum haka maganin zai fara aiki."

"Wadda kuma ake sa wa a cikin mahaifa, ba ta hana ƙwai ya zo, idan ƙwan ya zo, sai da ya wuce, kuma wacewarsa na bata tafiyar al'ada, kuma yana haifa da ciwon mara."

"Kuma tunda yana da wani zare, wanda ake amfani da shi wajen tabbatar da cewa yana nan, wani lokaci idan mace ba ta da tsafta, wannan zaren na iya ɗauko abin da ke waje daga cikin gaban ta ya kawo cikin mahaifa kuma ya sa mata infection."

Batun rashin jituwa tsakanin mata da miji, su waɗannan magungunan ba su sanya haka in ji likitan, ya ce ƙara ƙarfin sha'awa ma yake.

Dr Kabir ya ba da shawarar cewa mata da miji su kasancewa suna magana da fahimtar junan da kuma daidaituwa da junansu kafin yanke wata shawara game da amfani da magungunan hana haihuwa.

"Wani lokaci, shi mijin ke tilastawa mace ta je tayi amfani da magungunan, kuma killa ita mace ba ta son ta yi, irin wannan ba za a sami jituwa ba."

"In dai ita tana son tayi ciki, shi kuma mijin bai so, kuma ba su yi maganar fahimta ba ko daidaitawa ba, dole a sami matsala ko canji a gida."