You are here: HomeAfricaBBC2023 07 17Article 1806365

BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

Me ya sa ƴan Najeriya ke rige-rigen shiga Kundin Bajinta na Guiness?

Hilda Baci ta ɗora tukwane a murhu ta shiga girke-girke babu ƙaƙƙautawa don ta kafa tarihi Hilda Baci ta ɗora tukwane a murhu ta shiga girke-girke babu ƙaƙƙautawa don ta kafa tarihi

A lokacin da kuka gama karanta wannan labarin, akwai yiwuwar wani ɗan Najeriya ya yi yunkurin kafa wani sabon tarihi a duniya cikin gaggawa, al`amarin da zai ɗauki hankali a ƙasar da ta fi kowacce yawan al`umma a Afirka.

Abu ne mai wuya a lissafo dukkan waɗanda suke ƙoƙarin yin fice a wani aiki a yanzu, amma akwai wani mutum da ya rera waƙoƙi har tsawon sa'o'i 200 akwai kuma wanda ya fashe da kuka ba ƙaƙƙautawa shi ma don ganin ya kafa tarihi,.

Kuma an samu wata mace da ta zauna a gida tsawon lokaci yayin da aka samu mai suyar dodon-koɗi duk dai daga cikin masu ƙoƙarin ganin sunansu ya shiga kundin tarihin.

Cikin watan Mayu a jihar Legas al`umma suka yi dandazo a wata unguwar masu ƙaramin karfi don ganin yadda Hilda Baci ta ɗora tukwane a murhu ta shiga girke-girke babu ƙaƙƙautawa don ta kafa tarihi.

Ta kwashe sa`o`i 100 tana girki, kodayake sa`o`i 93 Kundin Bajinta na Guiness ya tabbatar a matsayin lokacin da ta kwashe.

Tun daga wannan lokaci, kowacce rana sai an samu sabbin masu kafa tarihi don shiga kundin Guiness.

A ranar Talata masu tafiyar da Kundin na Guiness suka bukaci a dakatar da gasar kafa tarihin cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na twitter jim kaɗan bayan wasu mutane sun bayyana aniyar kafa wani sabon tarihin da ya haɗa da suyar fanke irin wanda ba a taɓa yi ba.

Wannan sanarwar ta biyo bayan irinta ta farko inda Kundin Bajintar na Guiness ya buƙaci jama`a su fara bin ka`idoji da farko.

Ana ganin wannan jan hankali an yi shi ne don ƴan Najeriya bayan wata ƙwararriya a fannin tausa ta yanke jiki ta faɗi yayin da ta ɗauki dogon lokaci tana tausa.

Amma matar ta bayyana cewar sa`o`i 50 da ta kwashe tana aikin tausa ba ƙaƙƙautawa sun isa a sanya ta cikin Kundin Bajintar duk da cewar ba ta bi ka`idojin ba.

Wannan hukunci da gwanar tausar ta yanke wa kanta, ya haifar da ƙaruwar masu neman kafa tarihi ta ko ina ba tare da neman izini daga Kundin Guiness ba.

Akwai wasu masu dafa abinci da aka gano sun kashe murhun girki don su kwanta su huta waɗanda tuni aka soke sunayensu.

Wakilin Kundin Guiness ya shaida wa BBC cewar akwai buƙatar masu son sunansu ya shiga Kundin su bi ka`idojin da aka tanada, ya kuma ƙara da bayyana yadda takardun neman izini daga Najeriya suka ƙaru.

Farominiyi Kemi wadda ta gwada kafa tarihin har sau biyu kafin Kundin Guiness ya dakatar da ita, ta bayyana cewar al`ummar Najeria mutane ne masu walwala da son nishaɗi, kuma suna amfani da damarmaki a lokutansu.

Duk da ba ta yi nasara ba, shirin suyar fanke ba ƙaƙƙautawa ya ƙara mata sha`awar sana`ar toye-toye.

Nan gaba a watan Satumba wani Malamin Makaranta mai suna John Obot zai ɗauki dogon lokaci ya na karatu.

Tuni ya samu sahalewar Kundin Guiness har ya fara shirye-shiryen yin nasara kan Rysbai Isakov ɗan kasar Kyrgyzstan wanda ya kwashe sa`o`i 124 yana karatu.

Mista Obot ya dauki aniyar yin karatu a fili na tsawon sa`o`i 140 a birnin Uyo da ke Kudancin Najeriya da nufin zaburar da al`umma su rungumi al`adar karatu.

Mista Obot ya ƙara da cewar ya yi takaicin yadda mahukuntan Jihar Ekiti suka haramta sumba a jihar bayan an samu waɗanda suka faɗi saboda yin sumba ta dogon lokaci don shiga Kundin Guiness.

Tembu Ebere mutumin da yake kukan kwanaki bakwai a jere, ya bayyana wa BBC cewar yana fama da ciwon kai da kumburin fuska ya kuma ƙara da cewar akwai lokacin da idanunsa suka daina gani har tsawon mintuna 45.

A yanzu dai ya ce ya rage sautin kukan, amma kuma ya ɗauki aniyar sai ya kammala duk da cewar bai nemi izinin Kundin Guiness ba kafin ya fara kukan.

Da dama daga cikin ƴan Najeriya waɗanda suke yi wa wannan al`amari kallon bakuwar al`ada sun bayyana Miss Baci a matsayin wadda ta bankaɗo gidan rina.

Yayin da Ms Baci ke tsaka da girke-girke daga cikin waɗanda suka jinjina mata akwai Mataimakin shugaban Ƙasa da gwamnan jihar Legas da kuma ƴar tseren gudu, Tobi Amusan.

Miss Baci ta sami kyautar tikitin jirgi don tafiye-tafiyen shekara ɗaya a Najeriya ta kuma samu tayin tallace-tallace daga kamfanoni.

Miss Baci ta shaida wa BBC cewar ya zama wajibi ta yi wani abu da zai ƙara fitowa da nagartar Najeriya tsakanin kasashe.