You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218613

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

Me ya sa ake ƙarancin ruwan famfo a manyan unguwannin Abuja?

An shafe fiye da kwana 10 wasu manyan unguwanni a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja na fama da matsalar ƙarancin ruwan famfo.

Unguwannin da lamarin ya fi shafa sun haɗa da Ushafa da Kubwa da Dutsen Alhaji da Katampe da wasu sassa na Jabi da Gwarinpa da wasu sassan Garki da sauran su.

Wannan lamari ba ƙaramin sanya mutanen yankunan cikin tasku ya yi ba, musamman waɗanda ba su da rijiyoyin burtsatse.

Hukumar kula da babban birnin tarayyar ta ce wani gagarumin gyara da ake yi a Madatsar Ruwa ta Usuma ne ya jawo lamarin.

Mazauna yankunan da dama sun shaida wa BBC cewa wannan ne karo na farko da aka taɓa ɗaukar tsawon lokaci irin haka ana fama da matsalar rashin ruwa.

Yaushe ruwan ya dauke?

Wasu mazauna unguwar Katampe Extension da ke kan hanyar Kubwa sun ce tun ranar Juma'a 19 ga watan Maris da daddare ruwan famfo ya ɗauke a unguwar.

"Yau kwana 11 kenan babu ma alamar dawowarsa. Ga shi ba mu da rijiyoyin burtsatse a gidaje da dama a nan yankin.

"Yanzu tattalin ruwa muke yi tamkar zam-zam. Ga hidimomin rayuwa duk sai da ruwa suke tafiya daidai.

"Gaskiya lamarin akwai matuƙar takura a gare mu," a cewar wani mazaunin unguwar.

A ina ake samun ruwan a yanzu?

Tuni dai mutane suka fara neman mafita kan wannan lamari ta hanyar ko dai samun ruwan daga maƙwabta masu rijiyoyin burtsatse ko saya.

Wata mazauniyar unguwar Kubwa ta ce a wasu lokutan kuma "sai dai mu saya daga tankar ma'aikatar ruwa wani lokacin a kan naira 5,000.

"Amma wasu lokutan har a kan naira 10,000 muke saya. To yaya za mu yi ai dole ne.

"Sannan ko na tankar ma kafin ka samu yakan dauki lokaci don abin da yawa layi ne sai ya zo kanka," a cewarta.

Mafitar gaggawa ga wannan lamari dai shi ne tona rijiyar burtsatse, amma shi kuma abu ne da ke buƙatar dumbin kuɗaɗe don aiwatar da shi.

Kuma a yanayin da ake ciki na "taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar nan ai batun tona burtsatse ma bai taso ba," a cewar wani magidanci a unguwar Katampe da bai so a ambaci sunansa ba.

Dama kuma hukumomi sun sha yin gargadi kan yawan tona rijiyoyin burtsaste a birnin, musamman shekara biyu da suka gabata bayan da aka samu motsin ƙasa mai karfi a wasu yankunan birnin.

Hukumomin sun ce yawan tona rijiyoyin da ake yi ne yake jawo irin wannan motsin kasa wanda ke da matukar illa ga muhalli.

Me gwamnati take yi?

Tun da farko dai hukumar samar da ruwa ta birnin tarayyar ta sanar da al'ummar yankunan cewa "wani gyara ake yi a Madatsar Ruwa ta Usuma da ke yankin Bwari.

"Injiniyoyinmu na aiki kai da fata don magance matsalar. Amma kafin sannan mutanen da ke buƙatar ruwa na iya tuntubar manajojin yankunansu don a kai musu a tankoki," a cewar sanarwar.

Sai dai duk da cewa hukumomin sun ce ruwan tankar kyauta ne, mazauna unguwannin da dama sun shaida wa BBC cewa saya suke yi.

Kazalika wata majiya ta shaida wa BBC cewa lalacewar wani babban bututun da ke isar da ruwa zuwa unguwannin ne ya jawo matsalar, kuma sai an sayo wani daga waje.

Hakan na nufin babu ranar dawo da ruwan kenan.

Join our Newsletter