You are here: HomeAfricaBBC2023 11 23Article 1886468

BBC Hausa of Thursday, 23 November 2023

Source: BBC

Me ya sa China ke rufewa tare da ruguza masallatai

Hoton alama Hoton alama

China na rufe masallatai tare da lalata su ko karɓe su domin mayar da su wuraren aikata wasu abubuwan na daban, kamar yadda rahoton hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Humun Right Watch ya yi zargi.

Rusau ɗin wani ɓangare ne na 'yunƙurin' kakkaɓe ayyukan addinin Musulunci a China, kamar yadda HRW ta bayyana.

Akwai kimanin Musulmai miliyan 20 a China, wadda a hukumance ba ta bin wani tsarin addini, amma dai takan ce za ta bayar da 'yancin gudanar da addini.

Masu sanya idanu, sun ce ana samun ƙaruwar ruguza tsarin addini a shekarun baya-bayan nan, inda China ke neman samun ƙarfin iko kan addinai.

BBC ta tuntuɓi ma'aikatar harkokin wajen China da ta addinai don jin bahasinsu game da rahoton na HRW.

"Rufe masallatai tare da lalata su ko karɓe su domin mayar da su wuraren aikata wasu abubuwa, wani yunƙuri ne na daƙile Musulunci a China," in ji Maya Wang, daraktan riƙo na ƙungiyar Human Rights Watch.

Rahoton ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafin bil-adama da aka aikata a kan Musulmai 'yan ƙabilar Uyghur da ke arewa maso yammacin yankin Xinjiang.

Zarge-zargen da China ta sha musantawa.

Mafi yawan Musulman China na zaune ne a arewa maso yammacin ƙasar, da suka haɗar da Xinjiang da Qinghai da Gansu da kuma Ningxia.

A ƙauyen Liaoqiao mai rinjayen Musulmai da ke yankin Ningxia mai cin gashin kai, an cire rufin masallaci shida, kamar yadda HRW ta bayyana, inda aka lalata wuraren salla na wasu mutanen, in ji rahoton.

Hotunan tauraron ɗa'adam da kungiyar HRW ta samu sun nuna yadda aka mayar da wani ginin masallaci zuwa tsarin gine-ginen gargakiya na China tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

A yankin Ningxia kuwa kimanin masallatai 1,300 ne aka rufe ko aka mayar da su wasu abubuwa tun shekarar 2020, Kamar yadda Hannah Theaker, mai nazari kan musulman ƙasar, to shaida wa BBC.

Waɗannan alƙaluma na wakiltar kashi uku bisa huɗu na yawan masallatan yankin.

A ƙarƙashin shugabancin Xi Jinping jam'iyyar kwamunisanci ta nemi cakuɗa addini da manufofinta da kuma al'adun China.

A shekarar 2018, jam'iyyar ta wallafa wasu takardu da ke nuna iko ko mayar da masallatai wasu abubuwa.

Jam'iyyar ta umarci gwamnatin yankin da ta ''ruguza masallatai masu yawa, tare da rage gina masu ƙaranci

Ta samar da dokokin da ke nuna cewa ''dole a riƙa lura da ginawa da samar da kuɗin ginda masallatan:.

A baya, wannan danniya ta fi ƙamari ne a yankunan Tibet da Xinjiang, amma kuma a yanzu batun ya faɗaɗa zuwa wasu yankuna.

Akwai manyan ƙabilun musulunci a China. Huis da suka je China a karni na takwas a lokacin daular Tang.

Bangare na biyu shi ne ƙabilar Uyghurs, da mafi yawancinsu ke zaune a lardin Xinjiang.

Kusan kashi biyu bisa uku na masallatan Xianjiang an lalata su tun 2017, kamar yadda wani rahoto daga cibiyar nazarin tsare-tsare da Australiya ta bayyana.

Wani bidyo da ƙungiyar HRW ta tantance ya nuna yadda aka lalata wani wurin alwala a masallacin Liujiaguo da ke kudancin Ningxia jim kaɗan bayan an cire masa hasumiya da rufinsa.

A lardin Gansu, da ke kan iyaka da Ningxia, jami'ai sun sanar da rufe masallatan yankin, ko sauya musu fasali zuwa wani abu na daban.

A shekarar 2018 hukumomi sun haramta yara 'yan ƙasa da shekara 16 daga halartar wuraren ibada ko koyar da addini a Linxia, wani birni a lardin da aka fi sani da ''ƙaramar makka".

A 2019 wani rahoto da gidan talbijin na ƙaar ya nuna ya ce hukumomi sun sauya masallatai masu yawa zuwa wani abu na daban, kamar wuraren aiki, ko cibiyoyin al'adu.

Kafin gangamin 'tasirantar da China', Musulmai 'yan ƙabilar Hui, na samun tallafi daga bangarori da dama da ƙarfafa gwiwa daga kasar, in ji Dakta Theaker.

"Gangamin ya rage damar da mutum ke da shi na zama musulmi a China, tare da ƙara nauyi ga ƙasar kan ayyukan da suka shafi addini".

"Hakan na nuna yaddda ƙasar ke wayar da kan mutane kan ƙin jinin musulunci a ƙasar, kan haka ana buƙatar musulmai da su nuna kishi, tare da kallon duk wani katalanda daga waje a matsayin wata barazana", in ji ta.

Shugabannin ƙasashen Larabwa Musulmai a faɗin duniya na ta aza ayar tambaya tare da nuna fargaba ame da wannan mataki, kamar yadda daraktar ƙungiyar HRW, Elaine Pearson ta bayyana

Gangamin gwamnatin ya kuma shafi sauran ƙabilu da cibiyoyin da ke lura da addini.

Alal misali, a watannin bya-bayan nan China ta maye gurbin amfani da 'Tibet' da Xizang, a takardun dimplomasiyya, wanda sunan addini ne a yaren Mandarin.

Haka kuma hukumomin sun cire alamomin kuros a coci-coci, da kama fasto-fasto, tare kuma da janye litattafan Bible daga shafukan intanet.