You are here: HomeAfricaBBC2023 09 17Article 1845884

BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023

Source: BBC

Me ya sa Amurka ta damu da ƙawancen Putin da Kim Jong Un

Tutar Amurka da ta Koriya ta Kudu Tutar Amurka da ta Koriya ta Kudu

Amurka ta shafe gomman shekaru tana tunani yadda za ta magance matsalar Koriya ta Arewa.

To sai dai yanzu wata sabuwar matsalar da ke neman ɓullo wa Amurka ita ce sabon ƙawancen da shugabannin ƙasashen Koriya ta Arewa da Rasha ke son ƙullawa.

Ƙasashen Kim Jong Un da Vladimir Putin na da tarin takunkumai daga ƙasashen yamma, kuma Amurka na kallon sabon ƙawancen da suke fatan ƙullawa a matsayin wata barazana.

Kawo yanzu babu cikakken bayanin abin da sabin abokan ke son gina ƙawancen a kai, to sai dai babbar damuwar ita ce musayar bayanan fasaha, musamman fasahar makamin nukiliya ko ta jirgin ruwan ƙarƙashin teku da zai iya harba makaman nukiliya.

Kawo yanzu gwamnatin Amurka ta mayar da martani ta hanyar yi wa batun kalon raini, tana mai cewa mista Putin na nuna zaƙuwa ta hanyar yin abin da ta kira ''bara, ko roƙo'' domin taimaka wa ƙasarsa.

Amurkan ta kuma yi gargaɗi game da sabon ƙawancen, tana mai cewa za su ɗanɗana kuɗarsu.

To ko ya shugaban Amurka Joe Biden wanda ya daɗe yana fatan gina ƙawance da China, tare da yunƙurin kawo shugaban Koriya ta Arewa kan teburin sulhu?

'Lokacin gaisuwa'

A lokacin da Mista Biden ya ziyarci birnin Seoul cikin shekarar da ta gabata, 'yan Jarida sun tambaye shi ko yana da saƙo ga Mista Kim? , sai ya ce ''yanzu lokacin gaisuwa ne"

"Mista Biden ya buɗe tattaunawar sulhu, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ke buƙata, wannan hanya ce ta bayyana hakan cikin raha." in ji Frank Aum, wani masanin yankin Asiya na cibiyar wanzar da zaman lafiya na Amurka.

Ya ce wannan wata dama ce da ta ƙara suɓucewa: An samu damarmakin tattaunawa masu yawa da suka suɓuce wa duka ɓangarorin biyu a cikin kusan shekara 70 da suka wuce, waɗanda su ne suka haifar da matsalar da ake ciki a halin yanzu.

Mista Kim bai nuna sha'awar tattaunawar ba. domi kuwa bai ce komai ba game da buƙatar tattauanawar sulhu ta baya-bayan nan da Amurka ta ce a shirye take a yi koyaushe a kuma a ko'ina.

To amma ya ci gaba da tabbatar da matsayinsa na ci gaba da ƙera makaman nukiliya.

Tun shekarar 2022 ya yi gwajin makaman fiye da 100, kuma sau biyu yana yunƙurin harba tauraron ɗa'adam, duk wannan ya yi a ne a lokacin da gwamnatinsa ke ƙarƙashin jerin takunkumai.

'Gaba da kuma ƙawance'

A shekarar 2017, Pyongyang ta yi iƙirarin ƙera bom ɗin haidurojin (hydrogen) da za a riƙa sanya wa cikin makaman nukiliya domin harbawa, lamarin da ya zama wani babban mataki a shirinta na nukiliya.

Shugaban Amurka na wannan lokacin Donald Trump ya yi wa Koriya ta Arewa barazana da gaba da ba a taɓa gani ba a duniya",

Daga baya ne Mista Kim ya bayyana kammala tattara sinadaran ƙera makamin nukiliya - barazanar da yake fatan za ta taimaka wajen janye masa tarin takunkuman da aka ƙaƙaba masa.

Daga baya Mista Trump ya nemi su zauna teburin sulhu, inda mutanen biyu suka yi hannu da juna cikin watan Yunin 2018 a Singapore.

Baya ga wannan zaman shugabannin biyu sun sake yin zama har sau uku a Singapore da Hanoi da kuma kan iyakar Koriya, to amma duka zaman babu wanda ya haifar da wani ci gaba ba dangane da sasantawa.

To amma duk da haka sun samar da hulɗar diplomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Lokaci mafi muhimmanci game da tattaunawar shugabannin biyu, shi ne tattaunawar da suka yi a Hanoi cikin watan Fabrairun 2019.

A lokacin rahotonni sun ce Mista Trump ya ɗage wa Mista Kim wasu takunkumai na wucin-gadi domin sassauta masa, da nufin ita kuma Koriya ta Arewa ta sadaukar da babbar tashar nukiliyarta da ke Yongbyon.

Buƙatar da John Bolton - mai bai wa Trump shawara kan harkokin tsaro - ya ce Mista Kim ya yi watsi da ita.

An sake wani zaman a yankin DMZ da ta raba tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa.

Matsalar China

Tun bayan ganawar Trump da Kim, China ta fara nuna damuwa game da ganawar.

Mista Biden da gwamnatinsa sun yi babban yunƙuri ƙarfafa diplomasiyya da yankin Asiya, farawa da China, zuwa ƙarfafa ƙawance tare da ƙara tasirinta a yankin.

To sai dai ana ganin yunƙurin na gwmanatin Biden bai yi la'akari da Koriya ta Arewa ba, saboda ba ta yi wani yunƙuri na ganawa da shi ba.

Ita kuwa China - wadda ke da alaƙa da Moscow da Pyongyang - ta kasance wata babbar abar la'akari ga Amurka a lisafin da take kan Koriya ta Arewa.

Wani zai ce ƙawancen tamkar zaman lafiya ne ga yankin.

Ƙawance mai ƙarfi tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa za ta iya sanya Amurka ta girke makamanta a gabashin Asiya, abin da kuma China ba za so ba.

Shugaban China Xi Jinping ya yi koƙarin bayyana kansa a matsayin jagoran wanzar da zaman lafiya a faɗin duniya, inda ya lissafo yadda China za ta warware matsalar yakin Ukraine.

Ba ya so a kalle shi a matsayin mai goyon bayan Koriya ta Arewa ko Rasha ta ko wane fanni.

A ɗaya ɓangaren kuma, China za ta iya kallon ƙawancen Rasha da Koriya ta Arewa a matsayin hanyar kawar da tasirin Amurka a yankin Asiya.

"Ina ganin ƙawancen Koriya ta Arewa da China da kuma Rasha zai iya warware matsalar yaƙin cacar baka", in ji Mista Green.

"Ina ganin Mista Kim Jong Un zai faɗaɗa alaƙarsa da China da kuma Rasha domin samun abin da yake buƙata," in ji shi.