You are here: HomeAfricaBBC2023 07 26Article 1812809

BBC Hausa of Wednesday, 26 July 2023

Source: BBC

Me matakin da ƙasashe ke ɗauka na hana fiton hatsi zuwa ƙetare yake nufi?

Hoton alama Hoton alama

Jamhuriyar Nijar ta bi sahun ƙasashe kamar Indiya da ke ɗaukar matakin hana fitar da hatsin da ake nomawa a cikinsu, inda a baya-bayan nan ta haramta sayar da gero da shinkafar da ake samarwa a ƙasar zuwa waje.

Shinkafar da ake nomawa a Nijar ba ta da yawan a-zo-a-gani, amma ita ce ke samar da kashi ɗaya cikin huɗu na geron da ake taƙama da shi a Afirka ta Yamma.

Wani shugaban 'yan kasuwa, Alhaji Habu Ali ya ce hatsin da ake nomawa a ƙasar ba ya isar al'ummar Nijar, sannan mafi yawan shinkafar da ake ci, ana shigar da ita ne daga ƙetare.

Duk da haka, dillalan hatsi a Nijar kan yi safarar sa zuwa ƙasashe maƙwabta, a duk lokacin da suka fuskanci irin wannan amfanin gona yana daraja.

Sai dai a bana hukumomi sun yi gargaɗin cewa sai gida ta ƙoshi kafin a kai waje.

Barazanar auka wa matsalar ƙarancin abinci da ƙarin hauhawar farashi na tilasta wa ƙasashe ɗaukar matakin da ba a saba gani ba. Al'ummomin ƙasashen duniya da yawa ne ke fama da matsin tattalin arziƙi da tsadar rayuwa mafi tsanani a tarihi.

Karyewar yarjejeniyar safarar hatsi daga Ukraine bisa jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya, ga alama ta sake tsunduma ƙasashe cikin halin rashin tabbas ana tsaka da kukan hauhawar farashin da yaƙin Ukraine ya riga ya ta'azzara.

Ƙasashen Afirka da na Gabas ta Tsakiya masu sayen abinci mai matuƙar yawa daga Ukraine sun fara fuskantar ƙarancin sa tun cikin watan Fabrairun 2022, lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamaye cikin iyakar maƙwabciyar tata, bayan ta datse hatsi tan miliyan 20 da za a yi safara zuwa ƙetare a tashoshin ruwan Bahar Aswad.

A makon jiyan kuma Indiya, ƙasar da ta fi fitar da shinkafa zuwa ƙasashen waje a duniya, ta dakatar da fiton farar shinkafar da ba basmati ba, a yunƙurinta na daƙile ƙarin tsadar abinci a cikin gida.

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya lalata amfanin gona a Indiya, inda farashin shinkafa ya tashi zuwa fiye da kashi 11% a cikin wata 12.

Kamar Indiya, hukumomin Nijar sun ce matakin hana fitar da gero da shinkafa zuwa maƙwabtan ƙasashe ya zama wajibi a wannan lokaci saboda kare al'ummarsu daga auka wa matsalar ƙarancin abinci.

Shinkafa a yanzu, tana ƙara zama abinci gidan-kowa a Nijar, yayin da gero ya fi tasiri a yankunan karkara.

Jihohin da mashahurin Kogin Isa ya ratsa kamar Niamey da Tillabery da Dosso da Diffa ne suka fi noman shinkafar da ake yi a cikin gida, Zinder da Dosso kuma sun fi yin fice wajen samar da gero.

Wasu alƙaluma sun ce Nijar ce ƙasa ta biyu mafi noman gero a Afirka ta Yamma, inda take samar da tan million 3.5 fiye da kashi 15% na geron da ake samarwa a ɗaukacin yankin.

Damunar a bara ta yi matuƙar albarka a Nijar, inda ta noma amfani dangin hantsi irinsu gero da dawa da masara da shinkafa da kuma alkama har kusan tan miliyan shida, ƙari a kan amfanin da ƙasar ta samu bara waccan.

Sai dai a bana, damuna ta zo a makare cikin sassa da dama na ƙasar, abin da ya sa hukumomi suka ɓullo da matakan rage zafin matsalar da za a iya fuskanta.

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya a watan Afrilu ya yi ƙiyasin cewa ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara biyar kusan miliyan ɗaya ne daga ƙasashen tsakiyar Sahel uku ke fuskantar ramewa a bana, yayin da iyaye ke fama da ƙarin tsadar abinci da matsalar rikice-rikice da kuma sauyin yanayi.

Alƙaluman sun ce Nijar ce, ƙasar da za ta fi fuskantar wannan matsala da ƙiyasin yara 430,000.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kuma yi hasashen cewa adadin mutanen da ba su da tabbatacciyar hanyar samun abinci mai aminci zai kai miliyan 48 daga watan Yunin bana zuwa Agusta a ɗaukacin yankin Sahel.

Yaya hakan zai shafi maƙwabtan ƙasashe kamar Najeriya?

Tuni dai, hukumomi a Najeriya suka hana shigar da shinkafa zuwa cikin ƙasar, a yunƙurinsu na ganin 'Giwar ta Afirka' ta iya dogaro da kanta wajen ciyar da al'ummarta.

Yawan shinkafar da ake kai wa ƙasar a shekarun baya daga ƙasashen Indiya da Thailand wadda akan yi fito ta cikin ƙasashe maƙwabtanta kamar Nijar, a yanzu ya yi matuƙar raguwa.

Ɗumbin kamfanonin gurza shinkafa ne suka buɗe a 'yan shekarun nan a cikin gida.

Sai dai duk da haka, al'ummar ƙasar na kokawa game da ƙarin tsadar wannan nau'in abinci da kuma rashin ingancin shinkafar musamman idan an kwatanta da ta ƙetare.

Harkokin ciniki musamman na kayan amfanin gona tsakanin Nijar da Najeriya, yana da girma a matakin da ba na ƙa'idance ba. Al'ummomin ƙasashen biyu har sukan ci kasuwanni tare a kan iyakokin ƙasashen juna.

"Ba za su ji daɗi ba, mu ma ba za mu ji daɗi ba," in ji wani dillalin hatsi a kasuwar Dawanau ta Kano.

Ƙwararru da wasu masu ruwa da tsaki kamar Alhaji Musa Uba Darki, dillalin hatsi a Dawanau sun yi gargaɗin cewa matakin hana fitar da amfanin hatsi kamar wanda Nijar da Indiya ke ɗauka, yana iya tsawwala farashi.

Ya ce matakin zai iya ƙara takura harkoki a kasuwannin hatsi na maƙwabtan ƙasashe kamar Najeriya.

Shugaban ƙungiyar ADDC-Wadata da ke kare masu sayayya a Nijar, Mamman Nouri ya ce matakin hana fitar da geron zuwa ƙetare zai taimaka wajen tabbatar da ganin an samu abinci kamar masara da hatsi da dawa da shinkafa a kasuwannin Nijar.

Amma a cewarsa, hakan bai wadatar ba, muddin ba a ɗauki matakin sayo ƙari daga waje ba. "Don gaskiya akwai matsala" in ji shi.

"Babu laihi a ɗauka, namu idan ya fita, to kuma shigo da shi daga wani wuri, zai yi wuya saboda inda aka saba kawowa, ƙasashen nan ne na kewayenmu. Kuma su ma cikin matsala suke".

Alhaji Mustapha Darki ya ce ko da yake dai ba su cika sayen gero daga Nijar ba, amma 'yan kasuwa kan shiga Najeriya su sayi amfanin gona kamar gero da masara da dawa.

"Tasirin dai kurum zai sake ɗaga frashi, amfanin gona zai iya sake tsada."

Ya bayyana fargabar cewa idan matakin ya haɗa har da wake, to hakan zai iya yin illa ga Najeriya, don kuwa a cewarsa, akasari sun dogara ne kan waken ƙasashen maƙwabta kamar Nijar don cike giɓin yawan buƙatar da ake da ita a ƙasar.