You are here: HomeAfricaBBC2023 09 05Article 1838630

BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

Me Najeriya za ta samu a shigarta ƙungiyar G20?

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugabannin ƙasashe da firaiministoci daga sassan duniya za su haɗu a taron ƙungiyar G20 na shekara-shekara, wanda za a yi a Delhi babban birnin Indiya tsakanin 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

Babban abin da za a tattauna a taron wannan shekarar shi ne cigaba mai ɗorewa, amma ana sa ran za a tattauna rikicin Ukraine a gefe guda.

Shugaban Indiya Narendra Modi ne ke jagorantar taron na wannan shekarar, kuma shi ne ya gayyaci shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zuwa taron.

A ganin wasu daga cikin shugabannin duniya, Najeriya na samun cigaban da ake buƙata kuma shi ya sa gayyatarta a wannan lokaci ba zai taɓa zama wani abin aibi ba.

Najeriya na duba yiwuwar miƙa buƙatarta ta zama mamba a ƙungiyar, wato za ta zama ƙasa ta biyu daga Nahiyar Afrika da ke ƙungiyar baya ga Afirka ta Kudu.

Shugaba Tinubu zai halarci taron "bayan katin gayyatar da ya samu daga Firaministan Indiya Narendra Modi," kamar yadda Abdul'aziz Abdul'aziz maitaimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai ya bayyana.

Sabuwar gwamnatin na son bai wa masu zuba jari na ƙasar waje kwarin gwiwar zuwa Najeriya domin su zuba kuɗaɗensu da zimmar samar da ayyukan yi, maimakon dogaro kan rancen kuɗi daga ƙasashen ketare.

Wannan zai taimaka mata wajen farfaɗo da tattalin arziƙinta da kuma biyan bashin da ake bin ta, da farfaɗo da darajar takardun kuɗinta na naira.

A gefe guda kuma ƙasar na fama da hauhawar farashin kayayyaki, da dai sauransu.

Wace ƙungiya ce G20?

Ƙungiyar G20 wata tawagar ƙasashe 20 ce waɗanda ke zaunawa su tattauna kan tattalin arziƙin duniya.

Su ne ke samar da kashi 85 cikin 100 na harkokin tattalin arziƙin duniya kuma su ne ke samar da kashi 75 cikin 100 na kasuwancin duniya.

Su ne ke da biyu cikin uku na al'umar duniya.

Mambobinta sun haɗa da Tarayyar Turai da kasashe 19 - Argentina da Australia da Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Japan, Mexico, Rasha, Saudiyya, Afirka ta Kudu, Koriya ta Kudu, Turkiyya, Birtaniya da kuma Amurka.

A kodayaushe akan gayyaci Sifaniya a matsayin baƙuwa ta musamman. Najeriya ma ta samu kanta cikin waɗanda aka gayyata a bana.

Me Najeriya za ta amfana daga G20

Shiga cikin G20 da Najeriya ke yunƙurin yi wani mataki ne da zai ƙara ɗaukaka darajar ƙungiyar.

Hakan zai sa ƙasar ta riƙa zama ƙugu da ƙugu da hamshaƙan kasashen duniya waɗanda karansu ya kai tsaiko ta fuskar cigaba da tattalin arziki, irinsu Amurka da Rasha da Burtaniya da dai sauransu.

Kasancewar Najeriya ƙasa ce da ke da fatan faɗaɗa harkokin masana'antu, babu shakka za ta amfana da G20 saboda mambobinta ne suka fi kowaɗanne kasashe a duniya yawan masana'antu.

Wasu daga cikin alfanun da Najeriyar za ta samu sun haɗa da:

Janyo hankalin masu zuba jari na ƙasashen ƙetare;

"Taron zai bayar da damar haɗuwar kasashe ido da ido, wanda hakan zai taimaka wa ƙasashen da suka je da ƙoƙon bararsu miƙa bukatunsu ga waɗanda suka je nema," in ji Lawal Habib Yahaya Malami a kwalejin fasaha da ke Kano.

Ya ce wuri ne da ƙasaitattun ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki ke halarta, da manyan ƙungiyoyin duniya irinsu Bankin Duniya da Asusun ba da lamuni na duniya.

"Sabbin manufofin gwamnatin Tinubu na da yiwuwar janyo hankalin masu zuba jari na ketare, duk da cewa sun jefa 'yan ƙasar cikin wani yanayi maras dadi.

"Ganin Najeriya na da arziƙi iri-iri da makamantan ƙasashen da ke G20 ke iya amfana zai iya ba su damar shiga ƙasar domin tabbatar da su ma an dama da su."

Yiwuwar yafe bashi

Cikin abubuwan da aka saba tattaunawa a 'yan shekarun nan har da yafe basuka da kuma samar da rangwame ga waɗanda abin ya yi wa katutu.

"Irin wannan bashin ya yi wa Najeriya yawa, ta ci ya iya har wuya, don haka da yiwuwar Bola Tinubu ya bi sawun tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo wajen neman a yafe wa ƙasar bashin da ya dabaibaye ta.

"Wannan sai ya fi kowanne daga cikin abubuwan da aka fi hasashen Najeriya za ta amfana da shi a wannan taro," in ji Lawal Habib Yahaya.

Me ake tattaunawa a taron G20

Abubuwan da ƙungiyar ke tattaunawa a 'yan shekarun nan ya zarce maganar ci gaban tattalin arziki, a yanzu tattaunawar na haɗawa da batun sauyin yanayi, da samar da makamashi mai dorewa da yafe basuka da maganar kuɗin haraji.

Akan samu sauyi a kowacce shekara, saboda ana samun sauyin shugabanci, wanda kowanne shugaba na zuwa da tasa manufar.

A 2022, Indonesiya ce ta shugabanci taron wanda aka yi a birnin Bali.

A wannan shekarar ta 2023, Indiya ce za ta karɓi baƙuncin wanda za a yi a Delhi, kuma zai mayar da hankali kan cigaba mai ɗorewa, da kuma hanyoyin taimaka wa haɓɓakar tattalin arziki tsakanin ƙasashen da suka ci gaba da masu tasowa.

Taron na taimakawa wajen haɗuwa ido da ido domin tattaunawa tsakanin shugabannin ƙasashe.

Fadar White House ta ce shugaban Amurka Joe Biden zai tattauna da shugabanni daya bayan daya kan yadda za a shawo kan matsalar sauyin yanayi, da rikicin Rasha da Ukraine, da kuma tattaunawa kan ƙungiyoyin duniya kamar su Bankin Duniya domin ganin yadda za a ci gaba da yaƙar talauci.